SUFRA DA KHUDRAH :
SUFRAH: Sufrah wani ruwa ne wanda ya yi kama da yalo-yalo, kamar ruwan qurji yake, wanda yake fitowa mata daga gabansu.
KHUDRAH: Shi kuma wannan wani ruwa ne wanda yake gauraye da jaja-jaja, kamar jini ne a haɗe da ruwa: ya fi kama da jini amma ba jini ba ne.
Wata takan wayi gari ta ga ruwa yalo-yalo ko jaja-jaja, wato ruwa a gauraye da yalo ko gauraye da ja. Shin waɗannan abubuwa guda biyu, menene hukuncinsu?
Malamai suka ce waɗannan abubuwa guda biyu suna da hali guda uku:
Wannan ruwa mai yalo-yalo ko jaja-jaja idan yana zubowa mace kafin ta fara haila, ba za ta gina hukunci a kansa ba. Ma’ana za ta ci gaba da sallah, tana yin tsarki, tana wanke shi. Misali, mace ce kafin jinin al’adarta ya zo mata, sai take ganin wannan alamar khudrah da sufrah tsawon kwana ɗaya ko biyu, ba za ta gina hukunci ta ce wannan al’ada ba ce, tunda ba ta fara al’adar ba.
Za ta ci gaba da yin sallah da azumi, ba za ta ɗauki hukuncin mai jinin al’ada ba. Saboda hadisin Ummu Aɗiyyah (رضي الله عنها) ta ce: “Mun kasance ba ma qirga khudrah da sufrah a bakin wani abu a wannan lokaci na bayan tsarki.”()
Idan tana tsakar jinin al’ada sai kuma ta ci gaba da ganin khudrah da sufrah ɗin, wato mace ce al’adarta kwana shida take yi, sai jini ya zo mata a kwana na ɗaya da na biyu da na uku. A kwana na huɗu kuma sai ya juye ya koma khudrah da sufrah, a wannan lokaci za ta ɗauka kwana na huɗu da na biyar ma duka jinin al’ada ne, domin ana tsaka da jinin al’ada sufrah da khudrah suka zo, don haka sai ta ɗauka jinin ne ya koma wannan kalar. Saboda haka sai ta ci gaba da ɗaukansa a matsayin jinin al’ada, tunda ana tsaka da yin jinin suka zo, kuma jinin bai ɗauke ba, shi ne ya ci gaba da zuwa. Sai ta ɗauka shi ma jinin al’ada ne ba za ta yi sallah ba har sai gabaki ɗaya ya ɗauke tare da jinin da khudrah da sufrah ɗin.
Bayan mace ta gama ala’darta, ta yi wanka, ta yi tsarki, tana sallah, sai kuma ga wannan khudrah da sufrah ɗin, wannan ita ma ba za ta daina sallah saboda shi ɗin ba, kamar yadda wanda ya zo kafin al’ada shi ma ba za ta daina sallah saboda shi ba. Haka bayan ta gama al’ada wanda ya zo ba za ta daina sallah saboda shi ba, sai ta ci gaba da yin ibadarta. Domin sai da ta gama tsarki ya zubo, ta ɗauka kawai lalura ce da ta zo mata wadda za ta dinga wankewa.
Kamar yadda ya zo a hadisi cewa: “Mata sun ce ba ma qirga khudrah da sufrah a wani abu bayan tsarki.”
A wata ruwayar, “Bayan mun yi tsarki ba ma qirga shi a matsayin da zai sa ko ya tsayar mana da ibada ko kuma ya sa mu daina yin ibada ɗin.”
Da kuma abin da ya tabbata na hadisin Al-qamah daga mahaifiyarsa, wadda ita kuma bararriya ce ga Nana A’ishah (رضي الله عنها) wadda ta ce, mata sun kasance suna aikowa Nana A’ishah da kwando. A cikin kwandon akwai auduga a cikin audugar kuma akwai alamar jinin haila. Sai ta ce musu kada ku yi gaggawa sai kun ga al-qassatul-baidha’a. Ita wannan qassatul baidha’a ɗin, ita ce alamar ɗauraya na qarewar jinin haila. Domin ba da mace tana gama jinin haila ne ta gama jini ba, ko dai ta ga gabanta ya bushe alamar babu jinin kwata-kwata, ko kuma ta tabbatar cewa wannan ɗauraya na ruwan ya zo, ta san ta gama al’adarta. Saboda haka sai ta yi wanka, ta ci gaba da yin sallah.
YA ALAMAR ƊAUKEWAR JININ HAILA TAKE?:
Alamomin da suke nuna cewa jinin al’ada ya ɗauke guda biyu ne:
Al-qassatul Baidha’a: Wannan wani ruwa ne da yake fitowa daga cikin gaban mace, wanda yake nuna jini ya xauke, ga ma alamar ɗauraya nan.
Al-jufuf: Wato bushewar gaba, shi ne mace ta ga gabanta ya bushe, ta sami auduga da almiski ta duba ta ga babu wani jini. Wannan auduga da almiski su ne za ta ɗan saka amma ba a cikin gabanta ba, a gefe za ta saka ta ɗan goggoge jinin. Domin ba a so mace ta dinga saka ɗanyatsanta ko auduga a gabanta. Sai ta goge waje-wajen ba ciki ba, domin ya ɗauke qarnin jinin sannan kuma domin kar ta cutu, saboda ba a saka turare a cikin gaba. Yakan saka mata su ji zafi kuma likitoci suna tsoratar da hakan. A gefe-gefe za ta saka ta goggoge, saboda qarnin jinin ya tafi wanda ake kiransa (miskuɗ ɗahara).
Allah shine masani
Zamu ci gaba insha Allah
0 Comments