LITTAFIN FIQHU DARASI NA SHIDA




IDAN HAILA TA ZO KWANA NAWA TAKE YI YADDA IDAN TA WUCE WAƊANNAN KWANAKIN ZA A ƊAUKA BA HAILA BA CE?

Wannan mas’ala ita ma malamai sun yi saɓani a kanta, ta iyakance kwanakin da mace za ta yi ta daina al’ada, ko kuma iya kwanakin da ala’da za ta yi, idan ta wuce wannan kwanakin za a ɗauka cewa ta fita daga al’ada.
Malamai na farko suka ce babu iyaka dangane da ƙarancin kwanakin al’ada, ko kuma mafi yawansa. Duk lokacin da mace ta ga jini ko da kuwa awa ɗaya ne ko kwana ɗaya, ko da daddare, ko da rana, ko mafi yawa ko mafi qaranci, wannan haila ce, idan kuma ya ɗauke shi kenan ta ɗauke.
Saboda haka, akan sami mata waɗansu suna yin al’ada kwana ɗaya kawai a wata, ko kwana biyu, ko uku a wata, ko biyar ko shida ko bakwai duk wata. Amma idan za ka tambayi mata dubu za ka samu cewa kusan kaso casa’in cikin ɗari za su ce ba sa wuce kwana shida ko bakwai, duk da wasu matan sukan wuce hakan. Wata takan yi kwana takwas, wata kwana tara, wata kwana goma kai har akwai masu yin kwana goma sha biyar. Kai har an sami mai yin kwana ashirin tana al’ada duk wata. Don haka a kowanne wata sai ta yi kwana ashirin tana zubar da jini, sannan ta yi kwana goma tana cikin tsarki.
Wata kuma rabi, duk wata za ta yi rabi, wato kenan akwai masu yin ɗaya bisa goman wata shi ne kwana uku. Akwai masu yin ɗaya bisa shidan wata suna yin jini shi ne kwana biyar, da masu yin ɗaya bisa huɗu na wata, shi ne sati guda suna jini, da masu yin biyu bisa uku na wata, wato kwana ashirin suna jinin al’ada . Haka Allah ﷻ Ya haliccesu; tun farawarsu haka suka fara kuma haka suke yi.
Saboda haka sai malamai suke ganin mafi ƙaranci ya kamata a yi masa iyaka tun da ba a sami hadisi ko aya da ta yiwa jinin al’ada iyaka ba dangane da mafi ƙarancinsa, ko kuma ta yi masa iyaka dangane da mafi yawansa. Wannan ya sa malamai suka yi saɓani wajen iyakance yawansa, kuma wannan ya ginu ne a kan bincike da tambayoyi da suka yi wa mata saboda a cikin malaman babu mai yin jinin al’ada ko mutum ɗaya. Don haka sun gina ne a kan tambayar matan da suke yin jinin al’ada, da kuma dogaro da suka yi a kan wasu nassoshin.
Saboda haka kowa a yankinsa sai ya tara mata da suke yankin ya tambaye su yaya jinin al’ada yake a tsakaninsu? Wata ta ce, malam ni kwana goma nake yi, wata ta ce kwana biyar take yi. Idan ya bincika ya samu a cikin mata dubu an sami xari takwas suka ce suna yin kwana shida, sai malam ya ɗauka cewa kwana shida shi ne mafi yawa, kuma shi ne abin da za a gina hukunci a kai. Ko kuma ya bincika mata dubu biyu ko dubu uku duk amsarsu ta zamo cewa babu wacce take wuce kwana goma sha biyar (15) sai malam ya ɗauka cewa, tun da dai an sami mace xaya a cikin dubu ita ce kaɗai take kaiwa kwana goma sha biyar, sai a ɗauka mafi tsawonsa shi ne kwana goma sha biyar. Don haka duk wannan iyaka da malamai suke yiwa jinin al’ada da kwana ɗaya ko biyu ko uku ko huɗu ko biyar ko sha biyar, ko idan ya wuce sha biyar ya zama ciwo, an gina shi ne a kan bincike da tambayoyi da ake yiwa mata da fahimta da ijtihadi, amma ba Allah ﷻ ko Annabinsa ﷺ ne suka iyakance shi a cikin aya ko hadisi ba. Waɗannan kwanaki duk bincike ne da ijtihadi na manyan malamai, Allah ﷻ Ya saka musu da alheri. Saboda haka ake samun bambance-bambance tsakanin fatawoyi da abin da ake faɗa da kuma abin da su matan suke yi. 
Saboda haka a taƙaice, haila ba ta da mafi ƙarancin kwanaki ta yadda za a ce ƙasa da shi ba haila ba ce. Haka kuma ba ta da matsakaitan kwanaki ta yadda za a ce sama da shi ba haila ba ne. Amma idan a gaba ɗaya watan jini yake zuba, an san kuma babu wata mata da za a ce kwana talatin take yin haila, ma’ana duk wata sai ta yi kwana talatin don haka kenan a shekara za ta yi kwana ɗari uku da kusan hamsin da shida tana yin jinin al’ada, wannan ka ga kenan jinin ma ba ya tsayawa kwata-kwata, ita wannan hukuncin ta daban. Za a yi bayanin wata mata da tai shekara shida a zamanin Annabi ﷺ jini yana zubar mata ba ya ɗaukewa, kuma ta je ta tambayi Annabi ﷺ a kan haka kuma ya ba ta mafita ta hanyar mayar da ita zuwa ga mafi yawan abin da mata suke yi na al’ada, shi ne kwana shida ko bakwai. An kasa matan zuwa kashi uku wanda za mu ji kowacce da bambance-bambancen da yake tsakanin su.
Saboda haka kenan a taƙaice, haila takan iya zama kwanaki kaɗan, kuma takan iya zama kwanaki da yawa. Matuqar jinin bai zarce da zuba har ƙarshen wata ba, za a yi masa hukunci a matsayin haila ne, sai idan mace za ta iya bambance kalar jinin haila da wanda ba na haila ba, kuma tana da al’adarta sananniya daga baya abin ya zo ya rikice mata ya qaru, sai ta koma kan al’adarta. 
A nan mata sun kasu kashi huɗu:
1. Akwai macen da tana da al’adarta sananniya. Misali, kwana shida take yi sai jini ya zo ya rikice mata ya qaru akan kwana shidan. Wannan sai ta koma kan al’adarta idan jini ya wuce qa’ida ta dinga lissafin kwanakin da take yi a baya.
2. Akwai matar da ba ta da al’ada sananniya, ko kwanaki sanannu, amma kuma tana iya bambamce kalar jinin hailar da wanda ba na hailar ba. Wannan sai ta yi amfani da wannan ilimi da take da shi na bambance jini. Da zarar ta ga jinin ya sauya, ta san yanzu ba na al’ada ba ne. Sai ta yi wanka ta ci gaba da sallah.
3. Wacce take tana da al’ada sananniya kuma tana iya bambance kalar jinin ko launinsa, sai ta yi amfani da al’adarta da bambance kalar jinin. Idan jinin ya sauya ya fita daga na al’ada ya koma na ciwo sai ta yi amfani da wannan basira da ilimi da Allah ﷻ Ya ba ta.
4. Wadda ba ta da al’ada sananniya, ko wasu kwanaki sanannu tun lokacin da aka haife ta, ko kuma ba ta iya bambance kalar jinin ba, sai ta koma mafi yawan abin da mata suke yi, shi ne kwana shida ko kwana bakwai. Duk wata idan kwana shida ya wuce sai ta yi wanka ta ci gaba da yin sallah, sai kuma wani watan. Haka za ta ci gaba da yi domin shi ne iya abin da za ta iya. Masu wannan magana sun kafa hujja da faxin Allah ﷻ cewa:
﴿ وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ المَحِيضِ قُلْ هُوَ أّذًي فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي المَحِيضِ وَلاَتَقْرَبُوا هُنَّ حَتَّى يَطْهُرْنَ ﴾ ()
Ma’ana: “Suna tambayar ka game da haila, ka ce cuta ne, wato qazanta ne, ku nisanci mata lokacin da suke jinin al’ada, (ku nisanci saduwa da su idan suna cikin jinin ala’da) har sai sun sami tsarki.”
Na ɗaya, a nan Allah ﷻ Ya alaƙanta nisantar mata a bisa samuwar jinin. Don haka duk lokacin da aka sami wannan jini, kwana xaya ne ko biyu, da daddare ko da rana, mafi qaranci daga kwana ɗaya ne ko mafi yawa daga kwana ɗaya, wajibi ne mutum ya nisanci matarsa. Don haka sai ya nuna cewa, hukuncin haila an gina shi ne a kan samuwar jinin, ba a kan yawan kwanakin ko ƙarancin su ba.
Na biyu, hadisin Nana Ai’shah (رضي الله عنها) da Manzon Allah ﷺ Ya ce: “Idan hailarki ta gabato, to ki daina sallah, idan ta ba da baya ki wanke jinin ki yi sallah.”
 A nan ma Annabi ﷺ ya gina hukuncin jinin al’ada ne a kan zuwansa ko ɗaukewarsa ba tare da la’akari da wasu kwanaki sanannu ba.
Na uku, hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) lokacin da ta yi jinin al’ada suna tare da Annabi ﷺ a lokacin Hajji, sai Annabi ﷺ ya ce: “Ki aikata abin da mai aikin Hajji yake aikatawa sai dai ba za ki yi ɗawafi da Xakin Allah ﷻ ba, sai kin yi tsarki.” 
A nan ma, Annabi ﷺ ya gina hukuncin jinin al’ada bisa samuwarsa, ba tare da sa wani lokaci sananne ba.
Sai dai idan mace ta ga jini ya zo qasa da kwanakin da ta saba yi na al’ada, ko kuma ya wuce wannan lokacin, a nan me ya kamata ta yi?
Ya kamata ta yi la’akari ta duba da kyau zai iya kasancewa hailar ne ya qaru. Zai iya kasancewa ba jinin hailar ba ne na cuta ne, ko kuma jini ne na rashin lafiya. Saboda haka, a nan sai ta yi bincike ta hanyar duba kalar jinin ko kuma duba al’adar da take yi kafin ta sami wannan lalura, domin mafi yawan mata suna yin kwana shida ne ko bakwai suna jinin al’ada, kamar yadda ya zo a hadisin Amratu bint Jahsh, Annabi ﷺ ya ce: “Ki yi jinin al’adarki a bisa ilimin Allah ﷻ kwana shida ko bakwai shi ne na mafi yawa ga mata, sannan ki wanke, ki yi wanka, ki sallaci kwana ashirin da huxu, ko kuma kwana ashirin da uku, idan kin xauki kwana bakwai za ki dinga yi duk wata, saboda jini yana zubar miki kullum sai ki mayar da shi kwana shida ba kya yin sallah. Bayan kwana shida sun wuce, sai ki yi wanka ki ci gaba da yin sallah. Kin ga a lokacin kin yi kwana ashirin da uku kenan kina yin sallah a watan. Kuma idan kin ɗauki kwana shida kin ga kenan za ki yi kwana ashirin da huɗu kina yin sallah, kwana shida kuma ba kya yin sallah, gwargwadon yadda mafi yawan mata suke yi.”
Zamu ci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments