LITTAFIN FIQHU DARASI NA SHA BAKWAI



ABUBUWAN DA SUKE JAWO WANKA:

Abubuwan da suke jawo a yi wankan ibada su ne:
 1. Fitar maniyyi a cikin bacci, ko a farke, daga namiji ko mace, ta hanyar lafiya da jin daɗi, saboda hadisin da ya ce, “Idan ruwa ya fita a yi wanka.” Wato idan ruwan maniyyi ya fita, a yi wankan janaba.

2. Idan mutum ya yi mafarki yana saduwa da mace, amma da ya farka babu alamar fitar maniyyi, babu wanka a kansa. 

3. Idan mutum ya yi mafarki yana saduwa da mace, bayan ya farka sai ya ga maniyyi a jikinsa, wajibi ya yi wanka. 

4. Idan ya tashi daga barci sai ya ga maniyyi a jikinsa, amma bai yi mafarkin saduwa ba, wajibi ya yi wanka, saboda samuwar maniyyi a tare da shi, wanda fitarsa ne yake jawo wanka. 

5. Idan mutum ya ga maniyyi a jikin kayansa, amma bai tuna lokacin da ya yi mafarki ba, sai ya yi wanka ya rama sallar da ya yi daga lokacin da ya kwanta wannan baccin da ya yi mafarkin. 

6. Saduwa tsakanin mace da namiji, ya shigar da gabansa a cikin gaban mace, wajibi su yi wanka ko da maniyyi bai fito ba, domin Manzon Allah ﷺ Ya ce, “Idan kaciya biyu suka haɗu wanka ya wajaba” () ko da maniyyi bai fito ba. 

7. Idan mutum ya rungumi matarsa suka yi wasa kawai babu saduwa, kuma maniyyi bai fito ba, babu wanka a kansu, saboda rashin samun dalilan da suke jawowa a yi wanka guda biyu: fitar maniyyi ko shigar kaciyar namiji cikin gaban mace. Idan ba a sami ɗayan biyun ba, babu wanka. 

8. Idan maniyyi ya fitowa mutum bayan ya yi wanka, wasu malamai suna ga babu buƙatar ya sake wanka, wankansa na farko ya isa. An ruwaito daga Zuhriy da Hasanul Basriy sun yi fatawa ga wanda maniyyi ya fito masa bayan ya gama wanka cewa babu buƙatar ya sake wanka. 

9. Idan maniyyi ya fitowa mutum ta hanyar rashin lafiya, ko wata larura, ko aka yi masa wata allura domin a ɗauki maniyyi a jikinsa, duka wannan babu buqatar yin wanka, saboda rashin fitar maniyyi ta hanyar sha'awa. 

10. Idan mutum ya ga wani abu a jikinsa, amma yana shakka maniyyi ne ko ba maniyyi ba ne sai ya shinshina. Idan ya sami yaƙini ko zato mai ƙarfi cewa maniyyi ne, sai ya yi wanka domin ya fita daga kokwanto.

11. Haramun ne mutum ya sadu da matarsa tana cikin jinin al'ada ko jinin biƙi, ko ya sadu da ita ta dubura, amma idan ya keta Shari'a ya yi, sai ya yi wanka, kuma ya yi nadama, ya yi kaffara, ya tuba. 

 12 Abin da yake jawo wanka shi ne ɗaukewar jinin al'ada. Idan mace ta gama jinin al'ada ta tabbatar ya ɗauke har ta ga alamar ɗaukewarsa, sai ta yi wanka kamar yadda ya gabata a baya a wankan ibada. 

 13. Shi ne jinin biƙi. Idan mace ta haihu, jinin da yake biyo baya ya ɗauke, sai ta yi wanka, kamar yadda ya gabata a wankan ibada. 

14. Idan Allah ﷻ Ya arzuta mutum da shiga addinin Musulunci, ya wajaba ya yi wanka na ibada, kamar yadda ya gabata da niyyar ya shigo Musulunci. Saboda wani mutum Ya musulunta, Manzon Allah ﷺ ya umarce shi ya yi wanka.() 

15. Wankan ranar Juma'a, domin ya je sallah cikin tsarki da tsafta.

16. Idan mutum ya mutu a yi masa wanka kafin a binne shi, sai wanda Shari'a ta ce ba a yi musu wanka, kamar wanda ya yi shahada a filin daga fi sabilillah.

AKWAI WASU ABUBUWA DA SUKE JAWOWA A YI WANKA AMMA BA WAJIBI BA NE:

 1. Wanka ranar idi guda biyu, na ƙaramar sallah, da na babbar sallah. Idan za a tafi idi a yi wanka tukunna. Baihaqi ya ruwaito daga Sayyidina Aliyyu (رضي الله عنه). 

2. Wanka domin shiga haramar aikin Hajji ko Umra. Idan alhaji ya isa miqati an so ya yi wanka kafin ya ɗaura ihraminsa. Wannan wankan shi ma mustahabbi ne.()

 3. Wanka domin tsayuwar Arfa. An so ranar tsayuwar Arfa a yi wanka kafin a isa filin Arfa, ko idan an isa kafin rana ta yi zawali. Saboda hadisin da aka ruwaito daga Sayyidina Aliyyu (رضي الله عنه) wani ya tambaye shi game da yin wanka sai ya ce masa ka yi wanka duk sanda ka ga dama. Sai mutumin ya ce ina nufin na ibada wanda ba wajibi ba. Sai ya ce masa ka yi wanka ranar Juma'a da ranar Arfa da ranar babbar sallah da ƙaramar sallah. (Baihaqi ya ruwaito. Sheikh Albani ya inganta shi). () 

4. Wanka domin shiga garin Makkah, saboda an ruwaito daga Abdullahi xan Umar (رضي الله عنهما) idan ya isa Makkah sai ya kwana a wani wuri da ake kira Ziɗuwan. Bayan ya wayi gari sai ya yi wanka sannan ya shiga garin Makkah, kuma ya ce haka ya gani Manzon Allah ﷺ ya yi. ( 

5. Wanka ga wanda ya yiwa mamaci wanka, saboda hadisin Abu Huraira (رضي الله عنه) da ya ce Manzon Allah ﷺ ya ce, “Duk wanda ya yiwa mamaci wanka shi ma sai ya yi wanka, wanda kuma ya xauke shi, ya yi alwala. () 

6. Yin wanka ga wanda ya farfaɗo daga suma, saboda haka ta faru da Manzon Allah ﷺ kuma ya yi wanka bayan ya farfaɗo.

7. Yin wanka ga wanda ya sadu da iyalansa kuma yana buƙatar sake komawa. An so ya yi wanka a tsakanin haka domin an ruwaito daga Abu Rafi'i (رضي الله عنه). Ya ce, Manzon Allah ﷺ ya kewaya matansa a dare ɗaya, kuma yana yin wanka a tsakani. Sai aka tambaye shi me ya sa ba za ka wadatu da wanka ɗaya ba? Sai ya ce, “Haka ya fi tsafta da daɗi da kuma tsarki.”  

8. Wanka ga mace mai larurar zubar da jinin cuta, duk sanda za ta yi sallah sai ta yi wanka. Saboda Ummu Habibah bnt Jahash (رضي الله عنها) ta gamu da larura na zubar jinin cuta sai Manzon Allah ﷺ Ya umarce ta da yin wanka duk sanda za ta yi sallah. 

9. An so idan mutum ya binne gawar wani makusancinsa wanda ba musulmi ba, ya yi wanka. Saboda hadisin Sayyidina Aliyyu (رضي الله عنه) da Manzon Allah ﷺ ya umarce shi da yin wanka, bayan ya gama binne mahaifinsa, Abu Ɗalib. Abu Dawud da Nasa'i (Jami’ul Usul na Sheikh Shu`aib Arna'uɗ). 

 10. Idan mutum yana da janaba sai ya zama ranar Juma'a ce, kuma ta dace da ranar Idi. Idan ya yi wanka ɗaya tare da niyyoyin duka waɗannan wankan ya isar masa a wajen wasu malaman. 

11. Idan jinin haila ya ɗaukewa mace kuma ga janaba a tare da ita, idan ta yi wanka ɗaya da niyya biyu ya wadatar, ba sai ta yi wanka biyu ba, a fatawar wasu malaman..  

12. Ya halatta mace da mijinta su yi wanka tare, kamar yadda Manzon Allah ﷺ yake wanka da iyalansa a wasu lokutan. 

Malam Aɗa'u ya ce, “Ya halatta ga mai janaba ya yi ƙaho, ya yanke farce ya aske gashin kansa, ko da bai yi alwala ba.” 

13. Idan mai janaba yana so ya yi bacci, an so ya yi wanka ko alwala ko taimama, amma wankan ya fi.
Allah ne masani
Za muci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments