LITTAFIN FIQHU DARASI NA 32



KARATUN SALLAH
A raka’ar farko, mai sallah zai karanta abubuwa guda huɗu, su ne:
1. Du’a’ul Istiftahi: Wato addu’ar buɗe sallah wanda mafi yawan mutane ba sa yin ta.
2. Ta’awizi wato neman tsarin Allah ﷻ.
3.Karatun Fatiha.      
 4. Karatun surah.

YADDA AKE WAƊANNAN KARATU GUDA HUƊU
A cikin raka’a goma sha bakwai da muke yi a sallar farilla kowacce rana guda shida ne kaɗai ake bayyana karatunsu. Za a yi karatun du’a’ul is’tif’tah da ta’awizi da Basmalah a ɓoye, sannan a raka’o’i biyun farko na sallalolin Magariba da Isha’i da kuma Asubah za a yi karatun Fatiha da sura a bayyane, yayin da a raka’o’i huɗu na sallar Azahar da huɗu na La’asar, duka ɓoyewa ake yi. Raka’a ɗaya ta ƙarshen Magariba, ana karatun Fatiha a ɓoye. A takaice, raka’o’i shida ne ake bayyana karatunsu daga cikin raka’o’i (17) da muke yi a kullum: biyun farko na Magariba da Isha’i sai kuma biyu na Asubah.
Ya kamata mu riƙe du’a’ul is’tif’tah da kyau, domin muna gayawa Allah ﷻ abubuwan da muke so Ya yi mana ne, kuma wannan addu’a ta zo kala-kala, amma biyu da aka fi yawan kawowa su ne kamar haka:

((اللَّهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ، اللَّهُمَّ نَقِّنِي مِنْ خَطَايَايَ كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ، اللَّهُمَّ اغْسِلْني مِنْ خَطَايَايَ، بِالثَّلْجِ وَالْماءِ وَالْبَرَدِ )) ().

Abu Huraira (رضي الله عنه) ya tambayi Annabi ﷺ cewa, Ya Rasulullahi idan kana cikin sallah sai in ji ka yi shiru, sannan daga baya sai in ji ka ci gaba da karatu, me yake faruwa Ya Rasulullah, babana da babata fansa ne a gare ka? Ba ni labarin wannan shirun da kake yi tsakanin kabbara da fara karatu. Sai Manzon Allah ﷺ ya faɗawa Abu Hurairata “Abin da nake cewa Allah Ka nisanta tsakanina da tsakanin kura-kuraina kamar yadda ka nisanta tsakanin gabas da yamma. Allah Ka tsarkake ni daga kura-kuraina kamar yadda ake tsarkake (wanke) fararen tufafi daga datti. Allah Ka wanke ni tas daga kura-kuraina da ruwan sanyi da ƙanƙara da raɓa.” A nan Annabi ﷺ mu yake koyawa saboda shi a wanke yake tas. Ta la’akari da wannan, wanda ya bar du’a’ul is’tif’tah (addu`ar buɗe sallah) ya tafka babbar asara duk da yin ta ba wajibi ba ne kamar yadda fuqaha’u suka ce. Amma wa zai bar wannan addu’ar mai ɗimbin falala, mu da muke cikin kura-kurai masu ɗimbin yawa? A tuna fa duk fa Allah ﷻ ake yiwa wannan, domin Shi ne mai wankin ba wani mala’ika ba. Waye zai bar wannan garaɓasar a ce Allah ﷻ Ya wanke ka da ruwan sanyi da raɓa?
 Ai mutum ya tsarkaka!

Ɗaya du’a’ul is’tif’tah ɗin, addu’a ce amma da harshen kirari kamar haka:
((سُبْحانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، وَتَبارَكَ اسْمُكَ، وَتَعَالَى جَدُّكَ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ)) (). 
Ma’ana: “Tsarki ya tabbata gare Ka ya Allah da godiyarKa, sunanKa ya yi albarka, matsayinKa Ya ɗaukaka, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.” Wanda ya yiwa Allah ﷻ yabo da kirari, ai buƙatarsa tana nan a ɓoye a ciki. Ma’ana, yabon nan da yake yiwa Allah ﷻ da kirarin da yake yi, shi ma akwai wata niyya a ransa ta cewa idan Allah ﷻ Ya amshi yabon nan da kirari za a ba shi wani abu da yake buƙata, a tsare shi daga abin da yake ƙi, wato godiya da roƙon iri kenan.

Liman da mamu za su yi wannan du’a’ul is’tif’tah ɗin, domin ai Abu Hurairah (رضي الله عنه) yana cikin mamu, kuma ya tambayi Annabi ﷺ. Akwai limaman da suke yin du’a’ul is’tif’tahi, akwai kuma waɗanda ba sa yi. Wani da ya yi kabbarar harama kawai sai ya fara da Alhamdulillahi Rabbil Alamina kai tsaye. Shi ya sa akwai matsala idan aka shiga sallah ba tare da an karanta du’a’ul is’tif’tahi ba, domin ba a nemi tsari daga sharrin shaiɗan ba, kafin a fara sallar kamar yadda Annabi ﷺ ya gaya mana. Idan aka tayar da sallah shaiɗan yakan zo ya shiga tsakanin sahu ya dinga faɗawa mutum tuna kaza, tuna kaza. Wani lokaci ma sai ka shiga sallah sannan za ka fara tunane-tunane ta yadda mutum ma bai san raka’a nawa yi ba gaba ɗaya, ko guda nawa aka sallata saura nawa, saboda hankalinsa ya tafi wani waje daban. Tun da shaiɗan yana yi mana wannan tsiyar, sai Annabi ﷺ ya koya mana wannan du’a’ul istiftah wacce garaɓasa da alheri da neman tsarin Allah ﷻ ce.

Akwai littattafai da za a iya samun waɗannan addu`oi kamar Hisnul Muslim wanda ya tattaro su cikin hadisai da dama kuma an fassara littafin zuwa Hausa da Turanci da ma wasu harsuna da dama.

TA’AWIZI (NEMAN TSARI)

Bayan karatun du’a’ul is’tif’tah, sai ta’awizi wanda shi ma a ɓoye ake yi. Ta’awizi shi ne neman tsarin Allah ﷻ kuma yana da sigogi iri-iri. Daga ciki akwai A’uzu billahi minash shaiɗanir rajim, saboda Allah ﷻ Ya ce: “Idan za ka karanta Alƙur’ani ka nemi tsarin Allah ﷻ daga shaiɗan abin jefewa.”

Wato ya ce,
((أعوذ بالله من الشيطن الرجيم))
Ko kuma ya ce,
((أعوذ بالله السميع العليم، من الشيطن الرجيم))
Ko kuma ya ce,
((أعوذ بالله السميع العليم، من الشيطن الرجيم، من حمزه ونفخه ونفثه)) () 

Waxannan ta’awizai guda uku wato mutum ya ce, “Allah ina neman tsarinKa Kai ne mai ji kuma masani daga shaiɗan jefaffe, da haukan da shaiɗan yake sakawa mutane, da kuma girman kai da yake sakawa mutum, da kuma tofin shaiɗan.” Tofin shaiɗan da busar shaiɗan da wasi-wasin shaiɗan, sai aka fassara su da ‘hauka’ da ‘rashin tunani’ da ‘girman kai’ da kuma kaucewa gaskiya wanda shaiɗan yake kimsawa ɗan Adam. Daga su ne ake neman tsarin Allah ﷻ. A dunƙule, akwai buƙatar yin wannan ta’awizi a cikin sallah.

An sami saɓani wajen yin Basmala ta yadda wasu suna yin ta a ɓoye wasu kuma a fili suke yin ta. amma yin ta a ɓoye yafi kwarin hujja.
Zamu ci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments