LITTAFIN FIQHU (DARASI NA 22)




DALILAI 45 AKAN MUHIMMANCIN SALLAH DA FALALARTA

An gina Musulunci a kan rukunnai guda biyar: kalmar shahada, sallah, zakkah, azumi da hajji ga wanda ya sami iko.
Abin da ake so ga musulmi shi ne ya girmama Allah ﷻ, ya ƙaunaci Allah ﷻ, ya yi ƙwaɗayin samun rahamar Allah ﷻ, ya ji tsoron gamuwa da azabar Allah ﷻ. Duka akwai waɗannan abubuwa baki ɗaya a cikin sallah.
Sallah ita ce rukuni na biyu daga cikin rukunan addinin Musulunci: idan babu sallah, babu addini.
1. Asalin kalmar sallah tana nufin addu'a, ita kuma addu'a ta kasu kashi biyu. Akwai addu'a ta roƙo, da kuma addu'a ta yabo, wato ko kana roƙon Allah ﷻ ko kuma kana yabonsa. Duk waɗannan abubuwa guda biyu akwai su a cikin sallah.
2. A cikin sallah akwai karatun Alqur'ani mai girma, maganar Allah ﷻ, kabbara, girmama Allah ﷻ, tasbihi, tsarkake Allah ﷻ, tahmidi, yabo ga Allah ﷻ, addu'a da roƙon Allah ﷻ, tahiyya, jinjinawa Allah ﷻ, yin salati ɗaya ga Annabi ﷺ Allah ﷻ zai yi maka salati goma, akwai ruku'u da sujjada, ƙanƙan da kai ga Allah ﷻ, da miƙa wuya. Don haka, sallah duka addu'a ce, ko roƙon Allah ﷻ, ko jinjinawa Allah ﷻ.
3.Sallah ibada ce da ta ƙunshi ayyukan da ake yi da baki, kamar karatun Fatiha da sura, kabbara, tahiyya, tasbihi, salati, addu'a, sallama, da kuma ayyukan da ake yi da gaɓɓai, kamar ruku'u, sujjada, zaman tahiyya, ɗagowa daga ruku'u, sujjada, da miƙewa, duka ana yi domin bauta da biyayya ga Allah ﷻ.
4.Yin sallah wajibi ne, a cikin Alqur'ani Mai Girma, a cikin ayoyi masu yawa, da cikin hadisai na Manzon Allah ﷺ masu tarin yawa. Haka dukkan malaman Musulunci sun haɗu a kan wajabcin sallah.
5. Sallah ita ce ginshiƙin addini, babu addini ga wanda ba ya sallah, saboda Manzon Allah ﷺ ya ce, “Tushen komai shi ne Musulunci, ginshiƙinsa kuwa ita ce sallah, ƙololuwar samansa shi ne jihadi. ”  
6. Sallah ita ce farkon abin da za a yi hisabi a kansa ranar alƙiyama. Idan ta yi kyau komai ya sami wucewa, idan kuwa sallah ta ɓaci, komai ya lalace.
7. Sallah ita ce abin da za a rasa a qarshen duniya, domin Manzon Allah ﷺ ya ce: “Farkon abin da za a ɗauke daga cikin mutane shi ne amana, qarshen abin da zai yi ragowa shi ne sallah, amma da yawa za ka ga mai sallah amma babu alkhairi tare da shi.” Sahihul Jami'i na Albani.
8. Sallah ita ce wasiyyar ƙarshe da Manzon Allah ﷺ ya yiwa al'ummarsa.() Musnad na Imamu Ahmad. 
9. Sallah ita ce mafi girman ibada a Musulunci bayan tauhidin kaɗaita Allah ﷻ
10. . Saboda girman sallah, sai da Manzon Allah ﷺ ya yi Isra'i da Mi'iraji, ya je da kansa ya karɓo, amma ragowar ibadu Jibrilu ne ya kawo.
12. Da farko Allah ﷻ Ya wajabta mana salloli hamsin, amma aka yi ta ragewa har ta dawo biyar, amma ladanta yana nan. Idan ka yi sallah biyar, Allah ﷻ zai ba ka ladan hamsin din.
13. Sallah ita ce ake yin ta a kowanne hali, kamar sallar zaman gida, sallar tafiya, sallar yaƙi, sallar mara lafiya, sallar tsoro. Ana yin sallah a tsaye, ko a zaune idan akwai larura, ko a kwance, ko da nuni gwargwadon yadda ta samu.
 14. Sallah ita ce ibadar da ake gabatarwa a duk lokacin da wani abu ya taso: idan za a yi roƙon ruwa, salla ake yi, idan wata ya yi nusan sallah ake yi, idan mutum ya rasu, sallah ake yi, a yi masa addu'a da dai sauransu.
15. Dukkan wasu lokuta masu muhimmanci a Musulunci, sallah ake yi. Idan Juma'a ta zo sallah ake yi, idan Idi ya zo, sallah ake yi, idan an je Makkah sallah ake yi, idan buƙatu sun ta so sallah ake yi. Akwai sallar neman zaɓin Allah ﷻ (is’tikhara) da sallar neman gafara (salatul is’tigfari) da sallar buqata (salatul haja). 
16. Saboda muhimmanci sallah ake fara koyawa yaro tun yana dan shekara bakwai. 17.Saboda mahimmancinta, babu wani uziri na rashin yin ta a kan lokaci, sai bacci ko mantuwa kawai. Shi ma ana farkawa ko tunawa sai a yi maza a yi ta: mutum ba shi da wani uziri a Shari'ah na rashin yin sallah a kan lokaci.
18. Wajibi ne ga dukkan mai iyali ya tabbatar suna sallah a kan lokaci, tare da samun ilmi a kan yadda ake sallah.
19. Duk wanda ba ya sallah, yana cikin hatsari babba, domin har akwai malaman da suke ganin
19. Ya zama kafiri, idan yana inkarin wajabcin sallah a kansa, ko yana ganin ba addini ba ne yin sallah, kuma duk wanda ba ya sallah da gangan,
20.. Ba za a aura masa musulma ba,
21. . Kuma ba zai yi wakilcin aure ba,
22 . Kuma ba za a ba shi renon yaro ba don kada ya koya masa rashin sallah,
23. . Kuma babu gado tsakaninsa da musulmi. 24. .Kuma idan ya yanka dabba ba za a ci ba, 25. .kuma ba za a bar shi ya shiga garin Makkah ba.
26.. Idan kuma ya mutu ba za a yi masa wanka ba,
27.Ba za a sa masa likkafani ba,
28. Ba za a yi masa sallah ba,
29. Ba za a yi masa addu'a ba,
30. Ba za a binne shi a maƙabartar musulmi ba.
31. Idan kuwa rashin yin sallah da kulawa da ita na sakaci ne da rinjayar Sheɗan, ya yi sallah wataran, wani lokaci kuma ba ya yi, wannan ya zama fasiƙi, kuma ana jiye masa tsoron mummunar cikawa da mummunar makoma da rashin jin daɗin rayuwa a nan duniya da kuma lahira, amma ba za a kafirta shi ba.
32. Manzon Allah ﷺ ya ce,( “Alƙawarin da yake tsakanina da ku shi ne sallah, wanda ya bar sallah ya aikata kafirci.” 
Manzon Allah ﷺ ya ce: “ Tsakanin mutum da tsakanin shirka da kafirci shi ne barin sallah. ” 
Malam Ibnul Qayyim ya ce, “Akwai dalilai qwarara har guda ashirin da biyu da suke tabbatar da kafircin wanda ya daina sallah, kuma kafirci babba ,“ (irin wanda ake ficewa daga Musulunci).
 33. Sallah tana hana aikata alfasha da munkari.
34. Idan mutum yana kulawa da sallah, za ka ga yana rage laifi da mummunan hali.
35. Sallah ita ce darajar aikin da ake gabatarwa kafin komai. Za a iya yanke komai a yi sallah, amma ba za a iya yanke sallah domin yin wani abu ba, idan ba tsarki ne ya warware ba.
36. Sallah tana gogewa mutum dukkan zunubansa, idan yana yin ta yadda ya kamata.
37. Sallah haske ce ga mai yin ta a duniya da lahira.
38. Sallah tana ƙara kyan fuska, annuri, kwarjini da muhibba.
39. Sallah tana jawo samun kariya daga maƙiya da mahassada.
40. Idan mutum ya tafi masallaci domin yin sallah, duk taku ɗaya ana kankare masa zunubi, dayan kuma ana ɗaukaka masa daraja. 41.Mala'iku suna yin salati da addu'a ga dukkan wanda yake zaune a masallaci yana jiran sallah.
42. Sallah ita ce ibadar da idan kana jiran a yi ta za a dinga rubuta maka lada, kamar kana cikin yin ta.
43. Kada musulmi ya yi sakaci ko wasa da sallah.
44. Dukkan abin da muke ciki, idan an kirawo sallah mu tsaya mu fara yin ta tukunna.
45. Kuma wajibi mu koyi yadda ake sallah a ilmance, da kuma a aikace, domin samun rabon duniya da lahira.
Allah ﷻ Ya ba mu dacewa. Amin.
Duba littafin sallah na Sheikh Al-Qahɗaniy mai suna Salatul-Mumini domin karin bayani.
صلاة المؤمن

Post a Comment

0 Comments