Idan Saurayi Yana Miki Waɗannan Ɗabi'un Yaudaranki Yake Yi:




Sau tari mata suna faɗawa hannun mayaudaran maza ba tare da sun fahimta ba. A lokacinda zasu ankara kuma tuni an gama da zuciuarsu yadda zasu daina gani da hangon yaudaran da har zasu iya kaucewa faɗawa tarkon mayaudaran mazan.
Ga wasu ɗabi'un da ya kamata mata su kula da su, waɗanda mayaudaran maza suke amfani dasu.


1: Ɓoyewa mutane abunda ke tsakaninku:

 Akasarin mazan da suke da ɗabi'a na yaudara basu cika son su fito fili ba su nuna soyayyarsu ga wacce suke so. Don haka da zaran kinga mai sonki na noƙewa baya so a san kuna soyayya wannan bada gaske yake sonki ba.

2: Babu ke a tsarin rayuwarsa: idan namiji na sonki da gaske zai rika maganar yadda yake so rayuwarku ya kasance bayan kunyi aure.

A kullum zancensa baya wuce yadda zai yi rayuwa dake a matsayin matarsa.

Amma da kinji mai sonki baya irin waɗannan fatan, buri da zaƙuwa, to ki tabbata kina soyayya ne da mayaudari.

3: Yawan kashe miki ƙudi: shi na mijin da zai aureki yafi maida hankalinsa ne aka yadda za ku kashe kudi wajen shirin aurenku. Amma shi mayaudari zai so yayi ta kashe miki kuɗi ne babu zancen ko tunananin tanadin aurenku.

Idan kika ga mai sonki yana miki wannan kashe kudin ba tare da la'akarin cewa ku kashe kudin akan shirin aurenku ba to rabuda shi kawai yaudaranki yake yi.


4:Bai kishinki: mayaudarin namiji baya kishi da wanda yasan yana sonki da aure, amma da zaran ya fahimci mai sonki irin manufa guda ne da shi anan ne zai nuna miki yana kishinki. Amma idan ya tabbatar aurenki wannan zai yi babu ruwansa da nuna kishinsa a kanki.

5: Yakan yaba ko kula wasu matan a gabanki: duk mayaudarin namiji baya kunya ko shakkar yaba wata macen ko kulata ko amsa waya a gaban wacce yake yaudara. Da zaran kin fahimci hakan wajen mai sonki to ki tabbatar fa ba da gaske yake son aurenki ba.

6: Zai riƙa ɓoye miki:Mayaudarin mai sonki zai riƙa ɓoye miki duk wata hanyar dayasan kina iya nemansa idan ya tashi kaucemiki. Don haka duk wasu abokansa da 'yan uwansa na kusa ba zai barki ki sansu ba.

7: Babu girmamawa tsakaninku: a farko farko zai riƙa nuna miki kulawa da girmamawa, amma da tafiya yayi tafiya zai soma miki wulaƙanci a zahiri ko kuma ta waya.

Don haka ki kula da zaran mai sonki yana miki hakan bada gaske yake sonki ba.

8: Bai damu da nemanki ba: Mayaudarin namiji babu ruwansa danemanki idan kuka kwana biyu. Ko a waya kika kira ko aika saƙon tex sai yaga dama zai ɗauka ko ya miki amsa. Haka kuma babu ruwansa da kiranki idan yaga mis call ɗiki.

9: Baida lokacinki: a duk lokacin da kika nemi ganinsa zai ce miki baida lokaci, aiki ko ya baki wani uzuri na daban. A kullum haka zai yi ta faɗamiki domin ki gaji ki rabu da shi.

10: Gabanki ne a gabansa: shi mayaudarin namiji babu abunda yasa a gabansa illa yadda zai yaudari mace mai sonsa ya samu yin zina da ita. Da farko ne zai soma miki zancen aure, amma daga lokcinda ya samu gabanki kullum burinsa ki ci gaba da bashi gabanki yanaci.

Allah Ya kare ƙannenmu, 'ya'yan mu da dukkanin muminai mata marasa aure da sharrin mayaudaran maza.

Post a Comment

0 Comments