HANYOYIN MAGANCE ISTIMNA'I ILLOLIN SA DA SUKE HAIFAR: WAYS TO CURE DISODERS CAUSED BY EXCESSIVE MASTURBATION.


HANYOYIN MAGANCE  ISTIMNA'I ILLOLIN SA DA SUKE HAIFAR:

WAYS TO CURE DISODERS CAUSED BY EXCESSIVE MASTURBATION.  



Kamar dai yanda na wallafa a post din kwanan baya inda na zaiyano illolin da yawan Istimana'i kan haifar ga jikin namiji wanda a wannan karon ba bukatar in sake rubutu akan matsalar sai dai bayani akan hanyoyin da za a bi dan samun waraka ga matsalolin da wannan dabi'a ta masturbation take haddasawa musamman ganin irin yawan sakonnin da nake samu ta bukatar hakan daga mabiyan wannan shafin.

Idan dai har yin istimna'i ya haifar maka da daya ko fiye da haka daga cikin wadannan matsalolin da zan zaiyana a kasa to akoi bukatar ka bi wadannan hanyoyin dan samun waraka.

1.Saurin inzali.(Premature ejaculation
)

2.Rashin karfin zakari.(soft and weak erection)

3.Digowar maniyi a yayin fitsari ko bayan gari(semen leakage)

4.Low libido (karamcin shawa
) kai zaka ji tamkar baka balaga ba.Baka da wata doguwar shawa a jiki.

5.Tsananin kasala (fatique)

6.Saurin manta abu ko riqe karatu (forgetfulness and lack of confidence)

7.Saurin konciyar zakari (short term erection)nan take zakari da ya tashi baya jimawa sai ya sake kwantawa.

8.Bayan gari mai tauri (constipation)

9.Kamkamcewar gaba (smallness of penis) kaikace na karamin yaro ne.

10.Rashin ruwan maniyi masu kauri (thin semen fluid)

Mataki na farko anan shi ne ka canza tsarin rayuwarka gabaki daya waton life style.

Ka nisanci duk wani abu da zai sa kayin istimna'i.
Magangannun batsane kalle kallen hotunan fitsara da dai makamantansu.

Mataki na biyu : Ka rinqa cin abinci mai gina jiki (balancediet) . A hakika abinci na daya daga cikin manya manyan abubuwa masu taka rawa ta musamman dan samarda jini da maniyi ga jikin dan adam.

Dan haka a rinka cin abinci mai daukeda sinadirran dake da alfano ga jiki,kama daga sinadiran dake inganta lafiyar koda,zuciya da qwaqwalwa gami da na lafiyar mazakutar namiji(reproductive system)

Abinci da dama da muke ci muna cine kawai dan maganin yunwa amma a hakikanin gaskiya ba wata martaba yake yiwa jiki ba,baya daukeda nutritional values din da jiki ke bukata.Sai kaga anci abinci amma ana ta faman zuwa toilet saboda baya da wani amfani ga jiki.

Bawai sai abinci mai tsada keda vitamins ba,da dama muna ganin kamar sai mai hali ke iya cin abinci mai sinadiran dake gina jiki; wannan ba haka bane.Misali ga su zogale wallahi ba karamin taimakawa jiki ta ke yi ba.

Ga su ganyen alaiyafu da wake a rinka dafawa ana ci.

Ga kwai dafaffe duka qwara daya zuwa biyu ya wadatar ba abinci bane da za a zauna ayiwa cin tuwo abinda ake bukata kawai a rinqa ci akai akai amma bada yawa ba,dan shi abinci nau'in protein baya bukatar aci sa da yawa yana iya haifarda gudawa ko lalacewar ciki.
Kamar dangin kwai(eggs) meat (nama),madara(milk),kifi (fish),beans(wake).

Mataki na uku a rinka shan diyan itatuwa fiye da abincin da kake ci : Dalili anan jikinka ya rasa wasu muhimman sinadirai wadanda suna nan a cikin maniyin da kake ta zubarwa akai akai,wanda diyan itatuwan kawai zasu taimaka maka ka samu damar dawowa da wadannan sinadiran da ka rasa.

Haka kuma cutukka da dama da basa jin magani ana warkardasu ta yawan shan diyan itatuwa a hakika akoi fa'ida sosai ga haka.

Kamarsu lemu,cashew,abarba,kankana,karas,kwakwa da kuma shan ruwanta,ayaba, inabi,tuffa,da dai sauransu.

Harwa yau za a iya amfani dasu coconot oil
,cheese,peppers,zinc
,strawberries,flax seeds,kidney beans,da kuma avocadoes.

Mataki na 4 ka nemi wadannan magungunnan da ake kira da natural medicines wadanda basu da wani lahani a jiki dukansu daga tsirran itatuwa ake yinsu.

Pine pollen and maca root powder.
  
Tribulus trestiries.

Libido booster 

 Horny goat weed.

L-Arginine.

Zaka iya amfani da biyu ko uku a lokaci guda amma kada ka nemi wadanda ba su ba.ka tabbatar sune ka siya dan idan baka san products din ba to za a iya baka wadanda ba su ba wanda wani lahanine daban kuma ba zasu amfaneka ba.

Mataki na karshe sai a rinka motsa jiki akai akai,dan kada a ci a koshi a koma waje guda a jibge.

A daina shan kayan zaqi (sugary foods) da kayan maiqo.

A rinka samun isashen bacci.

Ina mai kara jan kunnuwan masu neman magani bafa kowane magani da kwashe kwashe iri iri kagani na yawo a kasuwa ko social media zaka kwasa kaje kayi ta sha ba,wallahi a kula a rinka neman shawara da kuma tattaunawa kan matsala kamin neman maganinta.kuma a zanka neman magani a inda aka san ciwo aka san magani.Ba inda ake wasa da lafiyar mutane ba.

Da fatar Allah yasa mu dace.


Post a Comment

0 Comments