Akwai ladubba da ake neman duk mai son Allah ﷻ ya amsa masa addu’arsa ya gabatar da su a yayin addu'ar da gabaninta da kuma bayanta. Su ne:
Ana son mai addu'a ya fuskanci Allah ﷻ da kyakkyawar niyyah mai tsarki, ya sakankance cewa Allah ﷻ ne kaɗai zai iya biya masa wannan buƙatun nasa shi kaɗai, don haka wajibi ne ya halarto faɗin Allah ﷻ inda yake cewa:
﴿ادْعُوا رَبَّكُمْ تَضَرُّعًا وَخُفْیَةً إِنَّهُ لاَیُحِبُّ الْمُعْتَدِینَ﴾ ()
Ma’ana: “Ku roƙi Allah ﷻ Ubangijinku kuna masu ƙanƙan da kai da bayyanar da tsoron Allah ﷻ da karyewar zuciya da mai da al'amari zuwa gare Shi a cikin zuciya, domin Allah ﷻ ba ya son masu ta’addanci da ƙetare iyaka.” An karɓo daga Mua'zu Ɗan Jabal رضي الله عنه ya ce, yayin da Ma’aiki ﷺ ya aike ni ƙasar yaman sai nace da shi, ka yi min wasiyya ya Ma’aikin Allah ﷺ, sai ya ce,
))أَخْلِصْ دِینَكَ یَكْفِیكَ الْعَمَلُ الْقَلِیلُ)) الحدیث أخرجه الحاكم وقال: صحیح الإسناد.
Ma’ana: “Ka tsarkake ibadarka ka nufaci Allah ﷻ da ita, idan ka yi haka aiki kaɗan sai ya wadatar da kai a wajen Allah ﷻ.” ()
Ya fara yabo da kirari ga Allah ﷻ, sai salati ga Annabi ﷺ saboda hadisin Fudhalata Bn Ubaid رضي الله عنه inda yake cewa, wata rana Manzon Allah ﷺ yana zaune sai wani mutum ya shigo ya yi sAllah, da ya gama sallar sai ya fara addu’a kai tsaye yana cewa, ya Allah ﷻ ka yi min gafara ka yi min rahma, sai Ma’aiki ﷺ ya ce da shi,
)) عَجِلْتَ أَیُّهَا الْمُصَلِّي، إِذَا صَلَّیْتَ فَقَعَدْتَّ فَاحْمَدِ ﷲ بِمَا هُوَ أَهْلُهُ وَصَلِّ عَلَيَّ ثُمَّ ادْعُهُ... قَالَ : ثُمَّ صَلَّى رَجُلٌ آَخَرَ بَعْدَ ذَلِكَ فَحَمِدَ اﷲ وَصَلَّى عَلَى النَّبِيِّ ﷺ فَقَالَ : أَیُّهَا الْمُصَلِّي ادْعُ تُجَبْ...)) () أخرجه أبو داود والترمذي والنسائي، وصححه الألباني في صحیح الجامع
Ma’ana: “Ya kai mai wannan sAllah ka gaggauta wannan addu’ar taka, (yadda ba za a karɓe ta ba) idan ka yi sAllah (kuma ka nufaci yin addu'a), idan ka zauna sai ka godewa Allah ﷻ ka yi masa kirari da irin abin da ya cancance shi, sannan ka yi salati a gare ni, sannan sai ka roƙi Allah ﷻ abin da kake so.”
To bayan wannan lokacin kuma sai wani mutum ya yi sAllah ya tsuguna zai yi addu’a, sai ya yi yabo ga Allah ﷻ ya yi kirari a gare shi, sannan ya yi salati ga Annabi ﷺ sai Ma’aiki ﷺ ya ce, “ya kai wannan mai sAllah roƙi Allah ﷻ abinda kake so za a amsa maka.”
Mutum ya yi addu’a yana mai sakankancewa, cewa Allah ﷻ zai karɓa masa, saboda hadisin Abu Hurairahh رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce,
)) ادْعُواْ ﷲ وَأَنْتُمْ مُوقِنُونَ بِالْإِجَابَةِ وَاعْلَمُواْ أَنَّ ﷲ لَا یَسْتَجِیبُ دُعَاءً مِن قَلْبٍ غَافِلٍ لَاهٍ)) () والحدیث حسن أخرجه الترمذي والحاكم .والطبراني وابن عدي
Ma’ana: “Ku roƙi Allah ﷻ kuna masu yaƙini da sakankancewa za a karɓa muku, ku sani cewa Allah ﷻ ba ya karɓar addu’a daga gafalalliyar zuciya rafkananniyya mai wasa.” wannan hadisin mai kyau ne.
Ana son mai addu’a ya yi nacin roƙon abin da yake son Allah ﷻ ya ba shi, saboda hadisin da yake cewa, “Lallai Allah ﷻ yana son masu na ci da dagewa a cikin addu’arsu.”
5- Ya halarto da zuciyarsa ga Allah ﷻ a lokacin da yake addu’ar, kada ya bari wani abu ya ɗauke hankalinsa ga barin jin Allah ﷻ a cikin zuciyarsa a lokacin da yake cikin addu’a, saboda hadisi Abu Hurairah رضي الله عنه wanda ya gabata kaɗan inda Ma’aiki ﷺ yake cewa,
)) وَاعْلَمُواْ أَنَّ ﷲ لَا یَسْتَجِیبُ دُعَاءً مِن قَلْبٍ غَافِلٍ لَاهٍ)) ()
Ma’ana: “Lallai ku sani cewa, Allah ﷻ ba ya amsa addu’a daga zuciyar wanda ya gafala rafkanne mai wasa.”
6- Ya riƙa yin addu’a a lokacin tsanani da lokacin yalwa, kada yaƙi yin addu’a sai an bashi, kamar yadda hadisi ya zo a kan hakan.
7- Kada mutum ya roƙi kowa sai Allah ﷻ, kamar yadda Ma’aiki ﷺ yake faɗa a hadisin Abdullahi Ɗan Abbas رضي الله عنه inda yake cewa,
))إِذَا سَأَلْتَ فَاسْأَلِ ﷲ وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسَتَعِنْ بِاﷲِ(( ()الحدیث أحمد، والترمذي وعبد بن حمید والطبراني والحاكم
Ma’ana: “Idan za ka yi roƙo ka roƙi Allah ﷻ, idan kuma za ka nemi taimako ka nemi taimakon Allah ﷻ...” Ka karanta hadisin har ƙarshensa.
8- Kada mutum ya yiwa kansa mummunar addu’a, ko ya yiwa ‘ya’yansa, ko kuma dukiyarsa, kamar yadda hadisin Ummu Salma ya nuna.
9- Kada mutum ya riƙa daga murya sama-sama a yayin addu’a, domin wanda kake kira ɗin ba kurma ba ne, ba kuma bebe ba ne. Kamar yadda Abu Musal Ash’ari رضي الله عنه yake cewa, mun dawo daga wani yaƙi tare da Ma’aiki ﷺ sai waɗansun mu suka hango garin madla’i sai suka ɗaga muryoyinsu sama-sama suna yin kabbara sai Ma’aiki ﷺ ya ce,
))إِنَّ رَبَّكُمْ لَیْسَ بِأَصَمَّ وَلَا غَائِبٍ هُوَ بَیْنَكُمْ وَبَیْنَ رُؤُوس رحالكم () ((
Ma’ana: “Lallai haƙiƙa Allah ﷻ Ubangijinku ba kurma ba ne, ba kuma a nesa yake ba, shi yana nan a tsakaninku da tsakanin sirdin raƙumanku.”
10- Mutum ya yarda da zunubinsa, ya nemi gafarar Allah ﷻ kuma ya san akwai ni’imar Allah ﷻ a kansa ya yi masa godiya.
11- Kada mutum ya kallafawa kansa gwanintar harshe a wajen addu’a, ma’ana ya ce dole sai ya yi addu'a da labarci.
Ya riƙa maimaita addu’a sau uku a lokaci ɗaya, wato idan ya faɗi buƙatarsa ya sake maimaita ta kamar yadda hadisi ya yi bayanin hakan.
Ya fuskanci Alƙibla idan zai yi addu’ar.
Ya daga hannayensa sama a yayin wasu addu’o’i kamar yyadda Anas Bn Malik رضي الله عنه yake cewa,
))رَأَیْتُ رَسُولَ اللهِ ﷺ یَرْفَعُ یَدَیْهِ فِي الدُّعَاءِ(( ()أخرجه مسلم وأبو داود والنسائي وابن خزیمة.
Ma’ana: “Na ga Manzon Allah ﷺ yana ɗaga hannayensa biyu a yayin addu’arsa.”
Ya yi alwala kafin ya shiga addu’ar.
Kada mutum ya wuce gona da iri a yayin addu'ar tasa, kamar yadda hadisi ya yi hani akan hakan.
Mutum ya fara yi wakansa addu’ar, wato idan addua'r za ta haɗa da waninsa, saboda hadisin Ubayyu Ɗan Ka’abu رضي الله عنه inda yake cewa,
))كَانَ رَسُولُ ﷲِ ﷺ إِذَا ذَكَرَ أَحَدًا فَدَعَا لَهُ بَدَأَ بِنَفْسِهِ)) ()
Ma’ana: “Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya tuna wani, kuma yana son ya yi masa addu’a, sai ya fara yiwa kansa addu’ar, sannan sai ya yiwa wancan ɗin daga baya.”
Ya yi tawassuli, ya yi kamun ƙafa da sunayen Allah ﷻ ko siffofinsa, ko da ƙaunarsa da yake yiwa Annabi ﷺ ko da salatin Annabi ﷺ ko kuma da wasu kyawawan ayyukan da ya yi don Allah ﷻ, kamar yadda wasu hadisai suka nuna hakan.
Ya kyautata abincinsa da abin shansa, ma'ana, abincinsa da abin shansa, su zamo na halal ne, kamar yadda hadisai suka nuna.
Kada mutum ya yi addu'a ta saɓo ko ta yanke zumunta kamar yadda hadisi ya gabata, a kan hakan.
Mutum ya riƙa yin umarani da kyakkyawan aiki ya riƙa hani da mummuna.
Mutum ya nisanci dukkanin saɓo karami da babba.
Ana so a yi addu'a a daren lailatil ƙadri, domin dare ne na amsa addu'a.
Tsakiyar dare ana amsa addu'a kamar yadda hadisi ya nuna hakan.
Ana amsa addu'a a tsakanin kiran sAllah da tayar da iƙama, kamar yadda hadisi ya nuna hakan.
Ana amsa addu'a a kowane lokaci da daddare.
Ana amsa addu'a a ƙarshen kiran kowacce sAllah ta farilla.
Ana amsa addu'a yayin saukar ruwan sama, kamar yadda hadisai suka nuna hakan.
Ana amsa addu'a a lokacin da aka yi sahu-sahu za a tafi yaƙin ɗaukaka kalmar Allah ﷻ da kuma yayin da aka yi sahun kafin a fara yaƙin, kamar yadda hadisai suka nuna hakan.
Ana amsa adu'a a ranar juma'a a wani lokaci musamman ma bayan sallar juma'ar zuwa faɗuwar rana.
Ana amsa addu'a yayin da za a sha ruwan zamzam tare da kyakkyawar niyyah, kamar yadda hadisi ya nuna.
Ana amsa addu'a a cikin sujjada, kamar yadda hadisi ya tabbata a kan hakan.
Idan mutum ya farka da daddare ya yi irin addu'ar da Ma’aiki ﷺ yake yi da daddare, za a amsa masa addu'arsa.
Ana amsa addu'ar wanda ya kwaikwayi irin addu'ar da Annabi ﷺ Yunusa عليه السلام ya yi, ita ce:
((لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ الظَّالِمِينَ)) .
Ana amsa adud'a a cikin tahiyyar sAllah ta ƙarshe, kamar yadda hadisi ya yi bayani a kan hakan.
Idan Musulmi ya yiwa ɗan uwansa Musulmi addu'a ba tare da ya sani ba, ita ma karɓaɓɓiyar addu'a ce, kamar yadda hadisi ya tabbatar da hakan.
Addu'ar ranar Arfa ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya tabbata a kan hakan.
Idan musulmai suka haɗu wasu suna addu'a wasu suna cewa amin, ita ma wannan addu'ar karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya yi bayani a kan hakan.
Ana amsa addu'a a yayin da mutum ya fuskanci Allah ﷻ da tsarkin zuciya, wato iklasi mai ƙarfi.
Addu'ar wanda aka zalunta a kan wanda ya zalunce shi, ita ma karɓanniya ce, kamar yadda ya tabbata a adisin Mu’az رضي الله عنه.
Addu'ar mahaifi ko mahaifiya ga ɗansu, ita ma karɓaɓɓiya ce nan take, kamar yadda hadisi ya tabbatar da hakan.
Addu'ar matafiyi a halin tafiya, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya tabbatar da hakan.
Addu'ar mai azumi a lokacin buɗa baki, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya tabbatar.
Addu'ar wanda ya shiga cikin matsananciyar buƙata, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar aya da yadda hadisi suka tabbatar da hakan.
Addu'ar shugaba adali, ita ma karɓaɓɓiya ce.
Addu'ar ɗa na kirki ga iyayensa, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya tabbatar da hakan.
Addu'a bayan an gama alwala, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya yi bayani a kan hakan.
Yin addu'a bayan an gama jifan sheɗan, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yada hadisi ya kawo.
Yin addu'a a cikin Ka'aba idan an sami damar shiga cikinta da kuma yin addu'a a cikin hijir-Isma'il, wato wannan ɗan kewayen da yake a jikin ɗakin Ka'aba, karɓaɓɓiya ce.
Yin addu'a a kan dutsen safa, ita ma karɓaɓɓiya ce.
Yin addu'a akan dutsen marwa, ita ma karɓaɓɓiya ce.
Yin addu'a a mash'aril haram, wato a muzdalifa, ita ma karɓaɓɓiya ce.
* * *
0 Comments