Wadannan kwanaki goma da muka shiga suna da matukar muhimmanci, a cikinsu ne dare mai albarka dare mai falala wato Lailatul Qadar yake.
LAILATUL QADAR Dare ne da ya yafi watanni dubu (1000) albarka. Kuma ana iya yin dace da shi a wadannan kwanaki na karshe.
ASARA ce ga musulmi ya bari kwanakin goman nan suka wuce bai ninka ayyukansa ba, muddin yana da lafiya.
Manzon Allah SAW) Yace:
"Duk wanda ya yi tsayuwar daren Lailatul Qadar yana mai imani da neman lada, an gafarta masa abin daya gabata na zunubansa"
(Bukhari da Muslim)
Manzon Allah (SAW)
Yana tashin iyalansa domin suyi harama suyi ibada kuma su sami albarka.
Nana Aisha; (RA) Tace:
"Ya Manzon Allah! Idan na samu tsayuwar Lailatul Qadr, me zan ce a cikinta?
ANNABI (SAW) Yace: Kice:
“Allahumma innaka ‘afuwwun tuhibbul ‘afwa fa’fu annee"
Ya Allah ka datar da mu a cikin wadannan kwanaki masu albarka, Allah kai ne mai afuwa ka yi mana afuwa, ka gafarta mana da iyayenmu da dukkan musulmi baki daya. Amin.
Asha ruwa lafiya.
#sisters & #brothers
0 Comments