Allah Gwani | Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da maɗaciya.




1. Jakar maɗaciya tana nan ɗamfare da hanta daga ƙasan hantar a ɓangaren dama daga sama a cikin ciki.

2. Hanta ce ke samar da ruwan maɗaciya wanda ke da launin kore ko kuma rawayar gwal, sannan ruwan maɗaciyar ya gangaro zuwa cikin jakar maɗaciya domin ajiya zuwa lokacin da za a buƙace shi.

3. Hanta na iya samar da ruwan maɗaciya da yawansa ya kai 800 – 1200 mL a kullum. A yayin da jakar maɗaciyar ke iya cin ruwan maɗaciyar da yawansa ya kai 50 mL bayan ta tace mafi yawan ruwan da ke ciki.

4. Ruwan maɗaciya ya ƙunshi kaso 97.6% ruwa zalla da kuma kaso 2.4% na gishirin maɗaciya da sauran ɓirɓishin ma'adanai da sauransu.

5. Gishirin maɗaciya shi ne jigon aikin maɗaciya a jikin ɗan Adam musamman wajen narka abinci.

6. Gishirin maɗaciya shi ne jigon sinadarin da ke narka ko markaɗa abinci ajin mai/kitse a cikin ƙaramin hanji har a mayar da shi zuwa yadda jiki zai iya zuƙe shi daga ƙaramin hanji zuwa sassan jiki. 

7. Gishirin maɗaciya na taimakawa wajen yi wa hanta ƙaimi domin samar da ruwan maɗaciya.

8. Har wa yau, gishirin maɗaciya na taimakawa wajen sauƙaƙa fitowar bayan-gida daga cikin babban hanji zuwa dubura. Kuma daga cikin ruwan maɗaciya ne bayan-gida ke samo launin ruwan ƙasa da yake da shi.

9. Tsakuwar maɗaciya: A yayin da kwalastirol ya hauhawa a jiki, kwalastirol na iya curewa ya haifar da matsalar da ake cewa tsakuwar maɗaciya wato "gallstone" a turance. Gishirin maɗaciya na taimakawa wajen magance curewar kwalastirol a cikin jakar maɗaciya.

10. Duk da ɗimbun alfanun maɗaciya ga jikin ɗan Adam, ana iya tiyatar cire jakar maɗaciyar idan aka samu matsalar tsakuwar maɗaciya kuma magunguna suka gaza magance tsakuwar.

***

Post a Comment

0 Comments