Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596
☏+2348037538596
Sirrinrikemiji@gmail.com
Sirinrikemiji@gmail.com
Islamic medicine center
'Yan'uwa Mata idan muka duba muka gani, zamu gano cewa gaba daya rayuwar aure hakuri ne a cikin ta, Kuma ita kanta kalmar aure, hakuri ne, Dan haka muddin ki Na Neman biyun bukata.
Tofa sai kin hada da hakuri, Saboda idan ki kayi aure, Zaki ga abubuwa da yawa, da ba ki sansu ba, Ko Kuma Baki saba ganin Sa ba, to Amma idan ki kayi hakuri, sai ki ga abin yazo ya wuce kamar ba'ayi ba, Kuma kiyi hakuri Mai yawa sosai.
Domin Zaki fi samun Nasara, idan Ko ki kayi gajen hakuri, to sai dai ma wasu al'amura su kara jagulewa, kiyi hakuri, Kama daga kansa shi Mai gidan, iyayensa,yayyinsa,kanansa,ya'yansa,da duk Wanda ya kamata.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
・HAKURI DA MIJI・
'yar'uwa ya zama miki dole, Don kuwa duk inda mace take,Tana karkashin da namiji,Kuma duk kyanki, kudinki, iliminki,da duk girman kanki, to dole ne ki ajiye gefe, ki bi mijinki, idan Har kin yarda aure bautar ubangiji ne, Kuma tunda mu ikon su ne,kamar yadda Allah yace to dole ne mu bi Abinda suke so, matukar bai sabawa shari'ah ba.
・ BIN SA SAU DA KAFA・
wannan ma ya zama mana dole, tunda Aljanna mu muke nema, Kuma Allah subhanahu wata'ala ya Fadi mana cewa, "Aljanna Ku Tana karkashin kafar su, Kuma ya umarce mu da bin dokar su, in dai Har ba shari'ah ta saba ma ba.
・ HAKURI DA DANGINSA DA KISHIYA・
wannan ma yana da muhimmanci, sannan Kuma duk abindaa zasu miki, kiyi hakuri, ki roki Allah mafita, kar Kuma ki dinga biye masu Ku Na cacan Baki, don kuwa duk Inda kishiya take da dangin miji, sai an yi hakuri zama da su.
・LADABI・
ki dinga yima mijinki ladabi, a duk Inda kike, domin ki nuna ma duniya irin zaman arzikin da ki ke yi dashi,Dan haka kar ki zama Mai gajiyawa ,ki zama mace Mai ladabi a duk Inda kika shiga.
0 Comments