--------------------------------------------------
Kamar yanda kuka sani, olsa kurji ne da ke samun tumbi ko hanjin dan adam.
Abubuwan da ke kawo olsa ko kuma suke iya tada OLSA su ne:
- shan maganin kashe ciwo ba akan ka'ida ba
- yawan cin abu mai yaji ko twanka
- yawan cin maiko
- yawan shan abu mai zafi
- yawan shan Lipton ko nescafe musamman wanda ba a saka madara ba.
- rashin cin abinci a cikin lokaci
- damuwa da yawan tunani.
MATAKAN DA YA KAMATA MAI OLSA YA DAUKA KAFIN WATAN AZUMI
--------------------------------------------------------
Ya kamata mai OLSA ya fara daukan matakai tun kafin shigowan watan Ramadan.
Daga cikin matakan da za'a iya dauka sun hada da:
- shan maganin OLSA a kan ka'ida
- shan magani sama da daya. Ma'ana Kada mutum ya sha magani kwara daya tilo domin OLSA na buƙatar magunguna biyu ko ukku
- shan maganin OLSA iya lokacin da a ka kayyade. Akwai maganin da ya kamata a sha har tsawon sati biyu, akwai na kwana goma. Duka ya kamata a shanye su.
- rage cin abin da ke iya tada olsa. Alal misali abu mai zafi, abu mai yaji, abu mai maiko dayawa.
MATAKAN DA YA KAMATA A DAUKA A CIKIN WATAN RAMADAN
---------------------------------------------------
- Yin sahur
- jinkirta sahur kamar yanda addini ya karantar
- kada a kwanta bayan cin abincin sahur, domin yin haka na iya tada OLSA
- shan maganin olsa bayan cin abincin sahur
- kada a ci abu mai yaji ko maiko ko lipton ko nescafe mara madara a lokacin sahur
- yin bude baki a cikin lokaci
- shan abu mai dan sanyi a lokacin bude baki
- cin dabino a lokacin bude baki
- shan maganin OLSA bayan bude baki
- kada a cika ciki sosai a zama daya bayan yin bude baki. A na son a ci abinci kadan kadan bayan mintuttuka ko awa
- shan kayan gona irin su ayaba. Kada a yi saurin shan laimu.
Idan an dauki wadannan matakan in shaa Allah za a samu sauƙin yin azumi musamman ga mai OLSA.
Akwai wadanda OLSA din su ya nada tsanani sosai ta yanda basa iya azumi. Ire-iren waɗannan mutane ya kamata su ga ma'aikatan lafiya.
Allah Ya sa mu dace.
Allah Ya gwada mana watan Ramadan mai albarka.
Asibiti A Tafin Hannun Ka
0 Comments