Chocolate Buns:
Kayan hadi:
Filawa kofi 1
Sikari 1/4 kofi
Butter cokali 2
Madara cokali 4
Garin cocoa cokali 2
Hoda 1/2 cokali
Vanilla 1/4 cokali
Kwai 2
Yadda ake yi:
A hada hoda, filawa da hodar cocoa a cakuda. A hada sikari, butter da kwai a buga har sai sunyi lakwab-lakwab. Sai a zuba madara ta ruwa da filebon vanilla essence tare da dan gishiri kadan, a motsa sosai sannan a zuba hadin su filawa dasu cocoa. A kwaba sosai sai ya zama kamar kwallo. Sai a yanka shi yadda ake so a gasa.
Cookies:
Kayan hadi :
Filawa kofi 2
Bota gwangwani 1
Sikari 1/2 kofi
Vanilla powder cokali 2
Jam 1/2 kwalba
Yadda ake yi :
A kada butter da sikari har se yayi lukub-lukub sai a rika zuba filawa da flavour ana juyawa har sai filawar ta zama kamar kwallo. A yanka a murza su kanana suyi rawon, ayi kananan hudoji da yar yatsa a rabi, a saka su duka akan farantin gashi a gasa. Idan sun gasu sai a dora mai hudojin akan marasa hudojin, a kuma zuba jam a cikin duka hudojin.
Coconut Biscuit:
Kayan hadi :
Kwakwa1
Filawa kofi 1
Rogo 1/4
Sikari kofi 1
Madara kofi 1
Kwai 2
Bota 1
Lemon tsami 1
Lemon zaki 2
Yadda ake yi:
A yanka, a fere a gurza kwakwa da rogo, a zuba madara, da ruwa a matsa lemon tsami da lemon zaki a cakuda sosai sannan a zuba kwai da fulawa, a cakuda har sai filawar ta hadu sannan a murza a yanka su yadda ake bukata a gasa a obin.
Chocolate Pudge
kayan hadi:
Sikari kofi 1
Madara mai zaki 1 (condensed milk )
Chakulate 1
Ruwa
Yadda ake yi :
A dora ruwa da sikari akan huta har sai ya narke se a zuba madara (condensed milk) a rika juyawa saboda kada tayi kamu, a cire daga kan wuta, bayan minti biyu a zuba chocolate (wadda aka gurza )
A kada su har sai yayi kauri sosai. A shafa butter a gwangwanin gashi (baking tin) a zuba hadin madara a ciki, a saka a firjin ya samu kamar awa biyar sai a fiddo a yanyanka.
0 Comments