Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
✦ Kankana
✦ Kwakwa
✦ Aya
✦ Dabino
✦ Garin citta
✦ Garin mazarkwaila
✦ Madara ta ruwa
Zaki samu kankananki mai kyau sai ki yayanka sai ki cire kwallon sai ki hada da sauran kayan hadin ki markada amma ban da madara bayan ki markada sai ki tace ki zuba madarar ki dunga sha.
Yadda Ake Hadin Garin Sallaja Ga Macen Da Take Fama Da Karancin Ni'ima:
Yar uwa idan kina fama da karancin ni'ima ko kina da matsalan rashin gamsar da maigida to ga dama ta samu.
Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
✹ Garin sallaja
✹ Garin gyada
✹ Garin habbatus sauda
✹ Garin dabino
✹ Garin aya
✹ Madarar peak
Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki hadesu guri guda ki gauraya har su hade sai ki dunga diban cokali biyu kina sha da madara.
Yadda Ake Hadin Tsumin Saiwar Kankana Don Samun Karin Ni'ima:
Yar uwa idan kina fama da matsalan rashin ni'ima to ga naki don wannan hadin dai sai alasan barka.
Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
★ Saiwar kankana
★ Saiwar zogale
★ Garin Kanunfari
★ Mazarkwaila
★ Zuma
Zaki samu saiwar kankana da na zogale sai ki tafasa idan ya tafasa sai ki tace sai ki maida ruwan kan wuta sai ki zuba mazarkwaila da kanunfari sai ki dafa na yan mintoci sai ki sauke ki tace sai ki zuba zumanki ki sa a frige don kar yayi saurin lalace ki sha.
Yadda Ake Hadin Kwababben Lalle Don Mtse Gaba Da Gamsar Da Maigida:
Zaki samu kayan hadi kamar haka;
☞ Garin Lalle
☞ Miski
☞ Man hulba
Zaki samu miski mai kyau sai ki hada da man hulba guri daya ki gauraya sai ki kawo garin lalle ki zuba a ciki ki kwaba sosai sai ki dunga diba kina matsi da shi bayan sallan isha idan ya samu kamar awa daya sai ki wanke da ruwan zafi.
0 Comments