Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* -Gyada
* -Kwakwa
* -Ridi
* -Dabino
* -Mazarkwaila
*Bayani;* Zaki samu gyadanki sai ki soya da ridi sama sama sai ki dauko saura kayan hadin sai ki hadasu guri daya sai ki dakasu dukka a turmi mai haka zaki ta dakawa har lokacin da yayi laushi kuma ya koma ya dunkule sai ki samu wuri mai kyau ki zuba ki dunga yanka ki damawa da nono kina sha, hmmmmm yar uwa idai kika juri shan wannan ai sai dai ki ba wata labari.
0 Comments