YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARFIN MAZA:



☞ MATSALALOLIN MA'AURATA:

Mafi yawanchin maza suna fama matsalar rashin karfin al'aura wanda hakan yakan sa su kasa biyama iyalansu bukata wanda yakanyi barazana sosai ga soyayyar su da zamantakewar aure.

.

1- A samu garin Habbatussaudaa kofi daya, garin Zaitun kofi daya, garin Tafarnuwa rabin kofi sai Zuma kofi biyu.

Sai a hada su waje daya, sai a dinga zuba cokali daya a shayi ba madara ana sha kullum sau daya, bayan an ci abinci.

2- A samu Alkama gwangwani hudu, garin Habbatussaudaa kofi daya.

Sai a gyara Alkamar, a nika ta, a hade su waje daya. Kullum a zuba cokali daya a rabin kofi na shayi ba madara a sha.

3- A dimanci shan zuma cokali biyu a cikin ruwan dumi kullum.

4- A samu saiwar Burqu da itacen Zumbur sai a hada su waje daya, kullum mai gida ya dinga sha sau biyu.

5- A samu danyen kwai kamar guda talatin. Kullum sai a dafa guda daya, sai ka cire kwanduwar, farin kwan kawai za ka ci tare da yankakkiyar albasa.

Kullum ka ci daya har kwan ya kare.

6- A samu gaban Ayu, sai a saka a cikin zuma har tsawon kwana bakwai. Idan ya juku sai ka dinga lasar zumar har ka shanye.

7- A samu Gurji da Ayaba, sai a markada ayi lemon juice a sa zuma mai gida ya dinga sha.

8- A samu busasshen Muruci da garin Kashe-Zaqi da Farin-Magani da Farin -Mauro. Sai a hada su waje daya a daka a tankade. Sai ka dinga zuba cokali daya a shayi ba madara kana sha kullum sau daya.

9- Ka samu Man Zaitun mai kyau, sai ka dinga shan cokali daya kullum kafin ka ci abinci.

10-A samu Muruci danye, sai a shanya ya bushe. Sai a hada da kanunfari da citta a daka. Se ka dinga zubawa a shayi ba madara kana sha.

11- A hada zangarniyar zogale da citta da kanumfari da masoro a daka. Sai ka dinga zubawa a abinci kana ci.

12- Ka dimanci cin Dafaffen Muruci.

13- Ka sayi gaban dan Maraqi ko dan Akuya wanda ba a yi wa fid'iya ba, a dafa maka da kayan kanshi ay maka miyar kuka da shi ka dinga ci.
.
14- Ka samu man Kanunfari ka dinga shafawa a gabanka kuma ka hada Man Kanunfari da Man Zaitun ka dinga shan cokali daya kullum.
.
15- Ka samu Giginya ai maka juice din ta ko ka dinga shanta a haka.
.
16- Shan rake shi ma yana taimakawa sosai ga da maza mata.

Sai kuma ka guji yawaita amfani da lemon tsami da kanwa don suna rage karfi kuma suna rage sha'awa.

Amma fa duk wannan zai maka amfani ne idan ya zamanto basur bai ci karfinka ba. Domin Basur yana hana namiji biyan bukatar aure kamar yadda sanyin infection yakewa mata. Indakuma akwai basir ko infection to lallai yakamata afara maganche su kafin ayi amfani da wadannan.

Post a Comment

0 Comments