Shi wanna hadi yana qara wa jiki kyau da kuma haske idan ana yi akai akai. yadda ake yin wannan hadi shi ne:
A samu madarar gari, a jika kadan da ruwa sannan sai a matse lemon tsami a ciki, a gauraya sosai sai a shafe fuska da hannu dama duk inda ake da bukatar yayi haske da laushi ko da duka jiki ne za a iya shafawa. Wannan hadi idan ana yin shi akai-akai za a ga yadda jiki zai yi kyau, laushi da kuma haske. Bayan an shafa, sai a barshi na tsawon minti biyar, sannan a wanke da ruwan dumi.
0 Comments