BI MOHAMMED LERE
– Shin Sanya tafarnuwa a kunne na rage radadi ko zafin ciwon kunnen?
Naturophatic medicine, wani tsarin kiwon lafiya ne da ya tanadi amfani da magungunan gargajiya wajen samun saukin rashin lafiya. Tsarin ya yi na’am da amfani da hanyoyin samun waraka da dama wadanda suka hada da amfani da wasu ganyayyaki, da tausa, da acupuncture – wani tsarin huda wasu sashen jiki da allura wanda ya samo asali daga kasar China, da motsa jiki da kuma shawarwari kan yadda mutum zai ci abinci mai gina jiki.
Tafarnuwa nau’in albasa ne da ake amfani da shi wajen kara dandanon abinci, maganin sanyi kamar yadda rahotannin game da tafarnuwa suka nuna. Ana iya balla shi a sami balli daga 10-20 a cikin guda daya.
Wani hoto da ake yadawa a shafukan yanar gizo ya nuna cewa idan kunnen mutum na ciwo, zai iya saka balli daya na tafarnuwar a ciki kuma zai warkar da cutar da ke damun kunnen. Bayan haka kuma wai, tafarnuwar na iya warkar da ciwon kai.
“Tafarnuwa na kawar da zafi da radadi a kunne, cututtuka a kunne da kuma ciwon kai sarai, kuma nan take. Mutum zai sanya tafarnuwa kawai a cikin kunne a tabbatar ya zauna sosai. Sannan sai a bar shi a kunnen har sai sadda zafi ko radadin ya dauke.”
Tantancewa
Dubawa ta fara da gudanar da bincike kan tafarnuwa domin gano irin alfanun da take da shi ga lafiyar dan adam. Daga nan ne ta gano wani rahoto a wani shafin kiwon lafiya mai suna Healthline da turanci. Rahoton ya ce lallai binciken kimiya ya nuna cewa tafarnuwa na da sinadaran da ke yaki da kwayoyin cuta, kuma yana hana kumburi da ma radadin jiki.
Rahoton ya kuma danganta binciken shi da wadansu rahotanni biyu wadanda suma Dubawa ta tantance.
Daya daga cikinsu wani binciken da aka gudanar ne a shekara ta 200, idan aka yi amfani da maganin ciwon kunnen da aka sarrafa da tafarnuwa da wasu ganyayyaki a kan yara 103 masu fama da ciwon kunne. Sakamakon binciken ya nuna cewa maganin kusan karfin shi daya da na asibiti wajen warkar da ciwon kunnen.
A bincike na biyu kuma an gano cewa idan har aka yi amfani da magungunan gargajiya kadai kusan sun fi aiki fiye da wadanda ake saye a asibiti wajen rage radadin ciwon kunne a kananan yara.
Dubawa ta kuma sake gudanar da bincike dangane da tafarnuwa ita kanta da ciwon kunne, inda ta gano wani binciken da aka yi a shekara ta 2019. Wannan binciken ya duba tasirin wasu sinadarai hudu da ake samu a tafarnuwa kan kwayoyin cutar da ke haddasa ciwon kunne. Sakamakon ya nuna cewa sinadarai biyu wadanda ake kira Allicin da SAC da turanci suna kashe kwayoyin cutar da ke haddasa ciwon kunnen ko da kuwa sinadaran ba yawa.
Daga Karshe
Bincike ya nuna cewa akwai wasu sinadarai dake kunshe cikin tafarnuwa da ke yaki da ciwon kunne ba a bada shawarar a rika sanya tafarnuwar ba tare da an sarrafa ta a cikin kunnuwa ba saboda babu wata hujja da ta nuna alfanun yin hakan a kimiyance.
Babu kwararan hujjoji da ke nuna cewa tafarnuwa na warkar da ciwon kunne duk da ko yana da matukar amfani wajen kara lafiya a jikin mutum, kamar yadda rahotannin binciken likitoci suka nuna.
SHARE.
0 Comments