SALLAR ASHAM, DA SHAFA’I DA WUTIRIDARASI NA 11




Sallolin tsayuwar dare, da sallar asham, da shafa'i da wutiri, su ne irin nafilfilin da ake so a yawaita yin su a daren watan Ramadan, tare da kyakkayawar niyyah, akwai nafila mai falala, ita ce raka'o'in Alfijir guda biyu, su ne waɗanda Ma’aiki ﷺ yake cewa, “Sun fi duniya da abin da ke cikin ta.” 
Daga ita kuma sai sallar walaha wadda hadisai daban-daban sun zo da kaifiyyar adadin ta, hadisi ya nuna za a iya yin ta raka’a biyu, ko raka’a huɗu, ko shida, ko takwas, ko raka’a goma sha biyu. 
Sannan akwai sallah kafin azahar raka’a huɗu, bayan azahar huɗu, ko kuma biyu kafin azahar, biyu bayan azahar, ko kuma huɗu kafin azahar, biyu bayan azahar, da kuma huɗu kafin la'asar, da biyu bayan magariba, da biyu bayan isha’i. 
Waɗannan nafiloli su ne waɗanda aka saba na yau da gobe a kullum, sannan akwai tsayuwar dare da kuma tsayuwar Ramadan, wanda ya haɗa da shafa'i da witri akwai alkhairi mai yawa a cikin yin sallolin dare wanda Allah ﷻ ya tabbatar da su a cikin Alqur’ani mai Girma, kuma sunnar Ma’aiki ﷺ ta tabbatar da su a cikin hadisai ingantattu. 
Allah ﷻ ya yaɓi wasu ma’abota littafi inda yake cewa:
﴿لَيْسُوا۟ سَوَآءًۗ مِّنْ أَهْلِ ٱلْكِتَٰبِ أُمَّةٌ قَآئِمَةٌ يَتْلُونَ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ ءَانَآءَ ٱلَّيْلِ وَهُمْ يَسْجُدُونَ۝﴾ ()
Ma’ana: “Ba duka suke ɗaya ba, akwai wata Al’umma daga ma’abota littafi waɗanda suke kan hanya madaidaiciya suna karanta ayoyin Allah ﷻ da tsakar dare suna masu yin sujjada.”     
Kuma Allah ﷻ Ya yaɓi nagartattun bayinsa inda yake cewa: 
﴿وَعِبَادُ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلَّذِينَ يَمْشُونَ عَلَى ٱلْأَرْضِ هَوْنًا وَإِذَا خَاطَبَهُمُ ٱلْجَٰهِلُونَ قَالُوا۟ سَلَٰمًا۝ وَٱلَّذِينَ يَبِيتُ��نَ لِرَبِّهِمْ سُجَّدًا وَقِيَٰمًا۝﴾ () 
Ma’ana: “Su dai bayin Allah ﷻ arrahmanu su ne waɗanda suke tafiya a bayan kasa a nitse idan, kuma wawaye sun yi musu maganganu (na wauta) sai su faɗi magana ta aminci. Kuma su ne masu kwana suna sujjada da tsayuwar dare sabo da neman yardar Ubangijinsu.” 
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلْمُزَّمِّلُ۝قُمِ ٱلَّيْلَ إِلَّا قَلِيلًا۝نِّصْفَهُۥٓ أَوِ ٱنقُصْ مِنْهُ قَلِيلًا۝أَوْ زِدْ عَلَيْهِ وَرَتِّلِ ٱلْقُرْءَانَ تَرْتِيلًا۝﴾ () 
Ma’ana: “Ya kai mai lulluɓa ta shi ka tsaya wa dare sai kaɗan za ka rage, rabin sa ko ka rage kaɗan daga ciki ko kuma ka yi ƙari a kai, sannan ka karanta Alqur’ani karantawa.”
﴿وَٱذْكُرِ ٱسْمَ رَبِّكَ بُكْرَةً وَأَصِيلًا ۝ وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَٱسْجُدْ لَهُۥ وَسَبِّحْهُ لَيْلًا طَ��ِيلًا ۝﴾ ()
Ma’ana: “Ka ambaci sunan Ubangijinka safe da yamma. Da daddare kuma ka yi sujjada a gare shi ka kuma yi tasbihi, tasbihi mai tsawo a gare shi.” 
A wani wurin inda Allah ﷻ yana yabon masu yin tsayuwar dare inda yake cewa:
﴿أَمَّنْ هُوَ قَٰنِتٌ ءَانَآءَ ٱلَّيْلِ سَاجِدًا وَقَآئِمًا يَحْذَرُ ٱلآخِرَةَ وَيَرْجُوا۟ رَحْمَةَ رَبِّهِۦۗ قُلْ هَلْ يَسْتَوِى ٱلَّذِينَ يَعْلَمُونَ وَٱلَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَۗ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُو۟لُوا۟ ٱلْأَلْبَٰبِ۝﴾ ()
Ma’ana: “Yanzun wanda yake shi mai yin ibada ne da tsakar dare yana sujjada, yana kuma tsayuwa yana kuma tsoron ranar lahira yana kuma kaunar rahamar ubangijin sa shin zai yi sai dai da wanda ba ya yi? Amma ba zai yi ba to ka ce, yanzu ashe waɗanda suke da sani za su yi daidai da waɗanda ba su sani ba?” Amsa a nan a'a ba za su yi daidai ba.
A wata ayar Allah ﷻ yana cewa: 
﴿كَانُوا۟ قَلِيلًا مِّنَ ٱلَّيْلِ مَا يَهْجَعُونَ ۝ وَبِٱلْأَسْحَارِ هُمْ يَسْتَغْفِرُونَ ۝ وَفِىٓ أَمْوَٰلِهِمْ حَقٌّ لِّلسَّآئِلِ وَٱلْمَحْرُومِ﴾ ()
Ma’ana: “Sun kasance a ɗan lokaci kaɗan ne suke kwantawa da daddare. A lokacin sahur kuma suna neman gafara, a kuma cikin dukiyoyin su sun ware wani haƙƙi da za su fitar domin masu neman taimako da kuma waɗanda suke da wadatar zu ci.” ​ 
Haka nan Allah ﷻ yana cewa:
﴿تَتَجَافَىٰ جُنُوبُهُمْ عَنِ ٱلْمَضَاجِعِ يَدْعُونَ رَبَّهُمْ خَوْفًا وَطَمَعًا وَمِمَّا رَزَقْنَٰهُمْ يُنفِقُونَ۝﴾ ()
Ma’ana: “Su ne waɗanda kuyaɓun jikinsu suke nisantar makwantan su, suna kiran Allah ﷻ da tsaro da kuma tsammani, kuma suna ciyarwa daga abin da aka arzuta su.”
An ruwato cewa Abu Hurairahh رضي الله عنه ya tambayi Ma’aiki ﷺ cewa, wace sAllah ce ta fi daraja a wajen Allah ﷻ a bayan farilla? Sai ya ce, “Yin sallah a tsakiyar dare.” ()
Haka nan Abdullahi Bn Salam رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sada zumunta, ku yi sallah da daddare, mutane suna barci, za ku shiga aljannar da aminci.” () 
Abu Malik Al’Ashja’i رضي الله عنه ya ce, lallai a cikin Aljannah akwai wasu ɗakuna ana hango cikinsu ta wajensu, kuma ana hango wajensu daga cikinsu, wato kamar gidan gilas suke, Allah ﷻ ya yi tanadin waɗannan gidaje ne ga waɗanda suka ciyar da abinci, suka yaɗa sallama, suka yi sallah da daddare mutane na barci.” ()
Daga Amru Bn Abasata رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Shi bawa yakan kasance yana kusa da Allah ﷻ ne a lokacin da dare ya tsala, don haka wanda ya sami ikon ya zamo daga cikin masu ambaton Allah ﷻ da yin sAllah a lokacin to ya kasance.” () 
A wani hadisin Abu Hurairahh رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Allah ya jiƙan mutumin da ya tashi yana sallah da daddare.” () 
Akwai wasu hadisan masu yawa da suke kwaɗaitar damu yin tsayuwar dare.
Kamar hadisin da Ma’aiki ﷺ yake cewa, “Ku riƙa yin tsayuwar dare domin ɗabi'a ce ta salihan bayi gabanin ku, domin yin hakan kusanci ne zuwa ga Allah ﷻ kuma yana wanke saɓo da kankare zunubai.”
* * * *

Post a Comment

0 Comments