Rubutu na biyu (2) game da Crypto Currency:




Bayan wadancan bayanai da muka gabatar masu yawan gaske, yau kuma zamu duba yadda zaka fara shiga harkokin kasuwancin Crypton.
Crypto Currency kamar dukiya ce dake kan kafar sadarwa, kuma wanda kowa ke iya mallaka matukan ya cika ka'idar da aka shinfida, wani zai ce yaya za'a yi a mallaki dukiya ta Online, dukiya ai abinda ake gani ake iya tabawa ne.
Wannan tunani ne da wasu 'yan uwa ko mutane da yawa suke yi, saboda yanzu ne ilimin yake isa zuwa gare su, da zaran sun samu wadataccen ilimin zasu daina tunanin zuwa wani sabon tunanin.
.
Idan ka lura zaka ga cewa, babban Malamin nan namu Dr. Isa Ali Pantami yana rike da ma'aikatar Sadarwa, da Turanci suna kiran ta da "Ministry of Communication and Digital Economy", tunda kaji ance "Digital Economy" daga nan zaka fara tunani cewa lallai fa akwai wani arziki ko dukiya dake zube acikin harkokin Online din nan.
Idan ka lura sati biyu da suka wuce hukumar SBC ta fitar da Kididdiga cewa ma'aikatar Sadarwa ta Sheikh Pantami ta samar ma Nigeriya da kudaden shiga fiye da ma'aikatar Man fetir da duniya take tinkaho dashi.
Abinda ba'a taba gani ba ace ga wata ma'aikata ta tara kudin da yafi na Ma'aikatar Man Fetur.
.
Wannan a babin misali ne na kawo mana, dan mu gane lallai fa akwai arziki a sama, kamar yadda Allah ya fadi acikin al-Qur'ani.
Shi Crypto Currency, kamar ka sayi fili ne (50 by 50) ko (50 by 100), ka saye shi a 1999 shekaru 21 da suka wuce akan Naira dubu goma.
Yanzu kuma bayan shekaru 20 kana so ka sayar, ba zai yi ka sayar dashi akan Naira dubu goman can da ka sayi filin a 1999 ba, watakil a yau zaka sayar dashi akan Naira dubu 'dari biyar ko ma miliyan 'daya.
.
Ya danganci wurin da filin yake, cikin gari ne ko daji, wurin da ake gine gine ne ko kauye ne.
Haka kuma Crypto Currency kamar ka sayi Buhun Masara ne yanzu, buhu hamsin (50) akan Naira dubu 9,000 misali, sai ka ajiye a damina ta sauka to zai kara daraja, idan ka tashi sayar dashi zaka iya samun sayar dashi a Naira dubu 15,000 koma sama da haka, akan kowane buhu ka samu Naira hudu kenan, misali ne wannan.
.
Idan ka sayi Coins na Crypto Currency a yau, zai iya tashi yau din ko gobe, da zaran kaga ya 'daga sama sai ka sayar dashi, kudin ka suzo kan wallet dinka, daga nan ka turo su zuwa account dinka.
Bari na bayar da Misali da wani Coins guda 'daya, sunan sa Doge coin:
A yau da muke magana yana Naira 28 ne, kowane guda 'daya.
Amma last month kowane guda 'daya yana Naira 13 ne, yanzu ba zaka same shi a Naira 13 ba sai dai 28, idan ya sauka yayi araha ne ka same shi a Naira 26 kafin ya sake mikewa bayan wasu awanni.
.
Ta yaya ake fara shiga harkokin Crypto Currency:
Ana farawa ne ta hanyar sauke application din 'daya daga cikin kamfanonin da suke harkar, zaka sauke zuwa kan wayar ka.
Kamfanonin suna da yawa sai wanda ka zaba, suna da application din su akan Play Store, da sauran su, daga cikin kamfanonin akwai na Nigeriya akwai na kasashen waje, akwai na Turai da na America da Asia, duk wanda ka dauko zaka iya amfani dashi matukan wayar ka Android ce.
.
Daga cikin kamfanonin ga wasu kamar haka:
1. Roqqu.
2. Bundle.
Wadannan biyun na 'yan Nigeriya ne, kuma suna da kyau kwarai da gaske.
3. Binance.
4. Trust Wallet.
5. Probit.
6. Bicona.
7. Crypto.Com
8. Luno.
9. Latoken.
Da sauran su, wadannan duk kamfanoni ne da suka shahara, kuma miliyoyin mutane suke amfani dasu suke wannan harkar ta Crypto Currency.
.
Idan kun lura, na fara kawo sunan wasu application guda biyu, (Roqqu) da (Bundle), wadannan Application din sun fi sauki ga 'dan koyo, sun fi saukin fahimta ga wanda yanzu yake so ya shiga harkar.
Idan kun lura a lamba ta uku na kawo sunan application na (Binance) ko BNB a takaice.
Shine application mafi kyau da inganci a harkar Crypto Currency a duniya (a sanin da nayi ma harkar a yanzu).
Sai dai yana da matsala guda uku:
Na farko yana da wahala ga 'dan koyo, idan ka bude shi da kyar ka gane me ake cewa idan baka saba harkar ba.
.
Na biyu yana da wahalan Registration, akwai 'daukan hoton kanka, wasu sukan yi kwana biyu ko sati biyu hoton bai 'dauku ba.
Sannan yana bukatan Network mai karfi idan kana son amfani da Binance application, idan kana wurin da ba network mai karfi toh gaskiya ranka zai baci dashi ne kawai.
Kuma mutane da yawa basa iya koyon sa ta Online dole sai ka hadu da wanda ya iya shi Face to face ya nuna maka.
Kamar Binance bai kamata mutum yace ka dauko ba tare da zai zauna ya koya maka shi ba, saboda wwahalar sa, amma idan ka iya shi yana da dadi kwarai.
Gashi nan👇

https://accounts.binance.cc/en/register?ref=75142476
.
Amma a babin shawara, ina bada shawara ga 'yan uwa suyi rijista kuma su dauko application na Roqqu:👇

https://app.roqqu.com/signup?ref=Kv1meOT5QVhz0ozVXvJG

.
Kowane application da irin Coins din da suke cikin sa, wani Application din yana da Coin da yawa kamar Binance da nayi magana akai.
Wanda yake son dauko application na Bundle kuma sai yabi ta cikin wannan link👇
https://referral.bundle.africa/rfrR
Yayi rijista sai yaje Play Store daga baya ya dauko application din.
.
Akwai Applications din da Coins din dake cikin su matsakaita ne, kamar Roqqu da Bundle, akwai wanda kuma Coins dinsa 'yan kadan ne, kamar Luno Application.
Misali, idan kana so ka sayi (Cardano Coins, ko ADA) ba zaka sami wannan Coin din akan Roqqu ba, sai dai akan Binance ko Bundle.
.
Wanda yake son 'dauko Binance, sai yabi nan 👇

https://accounts.binance.cc/en/register?ref=75142476

Amma kowane application zaka samu Bitcoin da Etherium acikin sa, saboda manyan Coins ne.
Kun ga kowane application yana da nasa amfanin da kuma nakasun sa..
.
Misali, kamar kaje kasuwar canjin kudi ne, idan kaje kana neman Dollar zaka same ta a kowane kasuwar canji, saboda babban kudi ne.
Amma ba lallai ka samu kudin kasar Belgium a kasuwar ba, saboda ba babban kudi bane, dan haka ba lallai a kawo shi kasuwar ba, amma nan gaba ana iya kawo shi.
Toh haka suma Coins din, ana iya kara yawan su akan application, amma kamfanonin ne suke karawa ba kai ba.
.
Amma akwai wadanda suke bada damar kayi Searching ka kara, kamar Trust Wallet application da wasun su.
Amma a babin shawara, ga wanda yake so yayi harkar Crypto, ya dace ya mallaki aqalla application guda uku, Roqqu, Bundle da Binance.
Ko Roqqu, Crypto.com da Binance.
Ko Bundle, Binance da Trust wallet.
.
Abu na karshe:
Duk wanda zai yi harkar Crypto dole ya kula wa wasu abubuwa guda hudu:
1. Phone number din da kayi rijista dashi.
2. Email din da kayi rijista.
3. Password din da ka sanya.
4. Correct account number, da bank name.
Wadannan sune key, ko manyan muhimman abubuwan da zaka kula dasu da farko.
Email dinka da kayi rijistan Crypto Currency application dashi kada ka yarda yayi expire, kada ka bari lambar da ka sanya ta bata ko ka rasa ta.
Amma dai mafi muhimmanci shine Email da password.
.
Tambaya ta gaba, yaya zan sanya kudi akai, ya zan sayi Coins, yaya zai sayar, yaya zan cire kudin zuwa account dina?
Yaya zan gane na samu Riba, ya zan gane na fadi, ko kasuwar ta karye?
Shin akwai wasu abubuwan da suke Haram acikin harkar domin na kiyaye?
Eh akwai wasu abubuwan da suke Haram a harkar, kuma zan bayyana su, zan nuna yadda za'a kauce musu.
.
Kamar yadda Riba ko Haram take shiga cikin kasuwancin Hatsi, ko kayan Miya haka akwai abubuwan da suke Haram acikin Crypto duk zan bayyana su nan gaba in sha Allah.
✍️
Rubutawa:
Abdul-Hadi Isah Ibrahim.

Post a Comment

0 Comments