RABE-RABEN AZUMI DARASI NA 7




Azumi ya kasu kashi-kashi, akwai azumi na wajibi da wanda ba na wajibi ba.
Azumi na wajibi ya kasu kashi-kashi. 
Kashi na farko: Azumin watan Ramadan.
Wanda yake hawa kan duk wanda ya cika sharaɗi bakwai :
Muslim
Baligi
Mai hankali
BA matafiyi ba
BA mara lafiya ba
BA mace mai jinin al'ada ba
BA mace mai jinin biƙi ba. 
Kashi na biyu: Azumin kaffara. Kamar kusan kai, zihari, rantsuwa, sakamakon farauta idan an kashe ta ana cikin aikin hajji, da makamantansu. 
Kashi na uku: Azumin bakance.
Kashi na huɗu: Shi ne azumin wanda ya yi Tamattu’i bai sami abin da zai yi hadaya da shi ba. 
Wato zai yi azumi uku a Makkah, sannan ya yi bakwai idan ya dawo gida. Waɗannan Azumummuka dukkansu wajibi ne a kan wanda suka hau kansa. 
Sannan shi kuma azumin da yake bana wajibi ba, ya kasu zuwa kaso biyu.
Kaso na farko: Azumin da ba a yi masa iyaka da adadi ko lokaci ba, wato shi ne azumin nafila wanda duk lokacin da mutum ya sami ikon yinsa a kowane lokaci zai iya yin abinsa in dai ba lokutan da aka hana yin azumi ba.
Kaso na biyu: Azumin da aka yi masa iyaka da lokaci ko adadi ko zamani, wannan shi ma ya kasu kashi tara (9). 
Daga ciki akwai waɗanda sau ɗaya suke maimaituwa a Shekara. Su ne kamar haka:
Yin azumi shida (6) a watan Shawwal. Wannan sau ɗaya kawai ake yin sa a Shekara.
Azumin ranar Arfa. Shi ma sau ɗaya ake yin sa a Shekara, amma fa ga wanda bai ɗauki niyyar aikin hajji ba.
Azumin ranar Ashura. Wannan shi ma sau ɗaya ake yin sa a Shekara, domin ita ranar sau ɗaya take zuwa a Shekara.
Azumin ranar tasu'a, wato azumin tara ga watan Al-Muharram, shi ma wannan sau ɗaya ake yin sa a Shekara.      
Don haka waɗannan kashe-kashen azumi guda huɗu, kowanensu ana yinsa ne sau ɗaya tak a Shekara. 
Haka kuma akwai azumin da yake maimaituwa a wata-wata. Misali, kamar azumin sha uku (13) da sha huɗu (14) da sha biyar (15) ga kowane wata. Shi ne ake ce masa azumin fararen ranaku. Domin shi ma irin wannan sau ɗaya yake maimaituwa a kowane wata. 
Sannan kuma akwai azumin da yake maimaituwa sati-sati. Misali, kamar azumin litinin da alhamis. Domin kowane sati ana samun litinin ɗaya, da alhamis ɗaya. Don haka azumin yana maimaituwa sau ɗaya ne a sati. 
Haka kuma akwai azumin da yake maimaituwa duk bayan kwana ɗaya. Shi ne azumin Annabi Dawud عليه السّلام kamar yadda Ma’aiki ﷺ Ya cewa, Abdullahi Ɗan Amru Ɗan As رضي الله عنهما cewa, ka yi azuminka a yau, gobe kuma ka huta ka ci abincinka. Wannan azumi ne da ake yinsa da fashin kwana ɗai-ɗai, wato ayi azumi yau gobe a huta, a yi azumi jibi gata a huta. Ma’ana, ana yin fashin kwana ɗai-ɗai. Waɗannan su ne rabe-raben azumi wanda Shari’a ta yarda a yisu. ()
Akwai azumin da yake iya zama haramun ne a yi shi. Misali, haramun ne mutum ya yi azumi a ranar idin ƙaramar sallah da idin babbar sallah . 
Haramun ne kai tsaye ga duk mutumin da ya san cewa gobe za a tashi da sallah shi kuma ya ɗauki azumin wannan wunin yana sane da gangan. Wanda duk yai haka ya saɓawa Allah ﷻ ya saɓawa Ma’aikin Allah ﷺ, kuma ya saɓawa haɗuwar kan malamai magabata na ƙwarai. 
Akwai azumin da yin sa makaruhi ne. Misali, mutum ya ɗauki azumi a ranar Arfa alhali kuma yana cikin aikin hajji. Wannan abin ƙyamata ne mutum yana aikin hajji kuma ya ɗauki azumi ranar Arfa. Domin Ma’aiki ﷺ ya yi aikin hajji amma ba a ga ya yi azumi a ranar Arfa ba. 
Sannan kuma za a iya kasa azumi zuwa kashi uku. 
Na farko: azumi na wajibi wanda Shari’a ta wajabta shi a kan duk wani Musulmi balagagge mai hankali; kamar azumin watan Ramadan, azumin da yake zama wajibi a kan mutum saboda wasu dalilai; kamar azumin bakance, azumin kaffarar kisan kai, ko na kaffarar zihari, ko na kaffarar rantsuwa ko na kaffarar shan azumi da gangan, sannan kuma da azumin ramuwa ga wanda ya sha azumin Ramadan saboda wata larura kamar jinin haila. 
Na biyu: azumi na mustahabbi, wato azumin da aka so Musulmi ya yi. Ma'anar mustahabbi shi ne idan ka yi shi za a ba ka lada, idan kuma ba ka yi ba, ba za a rubuta maka alhaki ba. 
To shi wannan azumin akwai wanda yake da iyakar lokaci da iyakar adadi. Akwai kuma wanda ba shi da lokaci ba shi da adadi. 
Mara adadi: kamar yadda Ma’aiki ﷺ yake yin azumi a cikin watan Sha’aban. Domin an samu hadisi cewa Manzon Allah ﷺ yana yin azumi a cikin watan Sha’aban. 
Saboda wani lokaci yakan yi azumi mai yawa a cikin watan ba tare da iyakance wani adadi ba. Wani lokaci kuma yakan wayi gari bai ɗauki azumin ba, amma idan ya shigo gida ya tambaya ko akwai wani abin da zai yi kalaci? Idan aka ce babu sai kawai ya ce to yanzu na yi niyyar azumi sai ya ci gaba da azuminsa. 
Mai adadi: Sai kuma azumin da ake yi na nafila wanda aka iyakance masa guri da lokaci da dadi, shi ne wanda muka kawo cewa yana azumtar ranar Arfa, da azumin tasu'a, wato azumin tara ga watan Al-Muharram da na ashura wato azumin goma ga watan Al-Muharram, da kuma azumin sitta shawwal, wato azumi shida (6) a cikin watan sAllah qarama. Sai kuma azumin fararen ranaku, wato sha uku (13) da sha huɗu (14) da sha biyar (15) ga kowane wata. Sannan da azumin ranar litinin da na alhamis da kuma azumin Annabi Dawud عليه السلام da makamantansu. 
Na uku: Azumin da ya haramta mutum ya yi azumi a waɗannan guraren kamar ranar idi biyu da ranar Arfa ga wanda yake aikin hajji. 
Kuma muna iya kasa lokutan azumi shi ma kashi-kashi; akwai lokutan da aka karhanta a yi azumi, akwai kuma lokutan da aka haramta a yi azumi. 
Wannan ya nuna mana a she azumi ya karkasu kashi-kashi, gwargwadon yadda hukunce-hukuncen Shari'a suka karkasa shi.

Post a Comment

0 Comments