Muhimman Abubuwa 10 Game Da Bijire Wa Dokar Ɗaura Bel Yayin Tuƙi.



1. Bel ɗin kujerar mota shi ne abu mafi bayar da cikakkiyar kariya a cikin mota wajen rage raunukan haɗuran ababen hawa.

2. Ɗaura bel ɗin kujerar mota yayin tuƙi na rage haɗarin mutuwa ga direbobi da fasinjoji mazauna gidan gaba da kaso arba'in da biyar zuwa kaso hamsin cikin ɗari(45 - 50%), da kuma kaso ashirin da biyar cikin ɗari(25%) ga fasinjoji mazauna baya.

3. Amfani da mazaunin killace yara a motoci na rage haɗarin mutuwa da kaso sittin cikin ɗari(60%).

4. Ƙara gudun tsere sa'a da kaso ɗaya(1%) tak fiye da matsakaicin gudu dai-dai yake da kaso huɗu(4%) na haɗarin mutuwa daga haɗarin abun hawa.

5. Rayuka miliyan 1.35 haɗuran ababen hawa ke lashewa duk shekara.

6. Tsakanin mutane miliyan 20 - 50 ke samun munanan raunukan da ke nakasa su a haɗuran ababen hawa.
 
7. Kaso casa'in da uku cikin ɗari(93%) na mace-mace daga haɗuran ababen hawa na faruwa ne a ƙasashe masu mafi ƙaranci da matsakaicin tattalin arziƙi.

8. Raunukan haɗuran ababen hawa ne ke gaba wajen lashe rayukan yara da matasa tsakanin shekaru 5 - 29.
 
9. Sanya hular kwano ga matuƙa babura na iya rage raunukan da ke haddasa mutuwa da kaso arba'in da tara cikin ɗari(49%), da kuma damar rage haɗarin samun raunukan ka da kaso sittin da tara cikin ɗari(69%).

10. Haɗuran ababen hawa na iya lashe kaso uku cikin ɗari(3%) na ƙimar hada-hadar cikin gida a mafi yawan ƙasashe.

Post a Comment

0 Comments