MATA MU FARKA DAGA BACCI YANZU NE LOKACIN KI:


 JIN DADIN MA'AURATA 

🌏www.sirrinrikemiji.com
✆ WhatsApp
☏+2348037538596
○ ```MATA MU FARKA DAGA BACCI YANZU NE LOKACIN KI``` ○

✾✾ ZAFAFAN SIRRIKAN MATA 50 YAKAMATA DUK WATA MACE TASAN WANNAN ✾✾

Duk Inda matar kwarai take, to sai an ga ta fita
daban da sauran mata, domin kuwa duk wani
abu da ake son mace ta hada, itama tana da
su , kuma duk Inda aka Kira ta da sunan mace,
to za ta amsa ba tare da ta yi shakkar
amsawar ba, za kuma a sameta kamar haka:

   ➽ WACCE BATA FITA SAI DA IZININ MIJINTA
             ❀••••21 POINT AGENDA••••❀

mace ta kwarai itace mai
﹄ hakuri
﹄ juriya
﹄ tsafta
﹄ iya kula da miji
﹄ mai kyaun hali
﹄ kawaici
⇛ ladabi
⇛ da kuma biyayya.

➽ sannan kuma itace wacce ba ta Bari mijinta ya ga abinda ba so daga gareta.

➽ itace mai kusanta da mijinta da tausayinsa.

➽ mai boye farin-cikinta a lokacin da mijinta ke cikin bakin ciki.

➽ sannan kuma mai iya sadaukarwa ga mijinta dukiyarta, idan bukatar hakan ta taso.

➽ mai kiyaye duk wata doka da mijinta ya
gindaya mata na shari'ah.

➽ mai nuna ma miji so na tsakani da Allah ba
don.
☛ kudinsa
☛kyau Ba.

✧ itace mai yawan yiwa mijinta addu'a a duk
Inda yake.

✧ sannan kuma mai girmama mijinta fiye da
kowa.

✧ kuma mai damuwa da mijinta a duk Inda
yake yana cikin ranta.

✧ mai juyo da hankalin mijinta,idan zai shiga
halaka.

✧ mai zama da mijinta in yana da shi, ko ba
shi da shi da hakuri da abinda ya bata.

✧ mai kokarin kyautata masa da kare
mutuncinsa.

✧ mai kokarin boye sirrinta da mijinta a duk
halin da suke ciki.

❊ mai rikon amana da addini.

❊ mai kishin mijinta da kuma yin mai addu'a.

❊ mai hangen nesa kuma kamila.

❊ mai tsare mutuncin mijinta a gaban idonsa
da bayan idonsa.

❊ mai iya lallaba mijinta ta samu biyan bukata cikin kwanciyar hankali, ba tare da ta je ga.

                  ✿ฺ´BOKA KO MALLAM`✿
ba
☛ mai iya mallakar mijinta, mallaka mai kyau
da ba mai iya juya shi sai ita.

. ▣••• TUNATARWA. •••▣

MATA mu rike wannan 21 point agenda saboda
muddin ki ka rikesu, to ko ba ki da kyau, kin
zama kyakkyawa, haka idan ki ka sakesu to ko
kina da kyau kin zama mummuna, domin ba za
ki zamo a cikin tashin hankali muddin ba ki ka
mallake su ba.

 ✿ KI BA MAI-GIDA KULAWA TA MUSAMMAN ✿

'yar-uwa ki kula, duk Inda namiji yake, to fa so
yake ki dinga tararaiyarsa kamar
➽ JINJIRI.

ma'ana ki dinga Lura da shi kamar yadda uwa
take Lura da yaronta, ki na ji da shi kamar
➽KARAMIN YARO.

ki na ba shi abinci a baki, ki dinga yi masa
➽WANKA.

Ki na yawan sumbatarsa da runguma
Sa masa kaya, shafa mai, da dai sauransu,
domin kuwa abin da yawa.

            ❀••• KI SAMU SINADARAI ••❀

' Yar-uwa ki samu sinadaranki, domin Kara
janyo hankalin mai-gida ta fannin:

☛ ABINCI.
☛ KAYAN SA KAMSHI A GIDA DA JIKI DA GIRKI
DA SAURANSU.

             🍲 SINADARAN GIRKI. 🍝

curry, thyme , onga , rayco , Maggi ,seasoning
powder , carrot cabbage , peas , green beans ,
green pepper , da sauransu , duk wadannan
sinadarai ne na.

                   ◈◞GYARAN ABINCI◟◈

   ✿✿✿ SINADARAN KAYAN JIKI ❀❀❀

Akwai
➜ roll on
➜ humra
➜ body spray
➜ handa cream
➜ body cream
➜ face cream da sauransu.

          | ☖ SINADARAN KAYAN BAYI ☖ |

kamar:
• dettol
◦ toilet flosher
◦ toilet air freshener
• bath fruit.

                  ❊・ (TUNATARWA) ・❊

'Yar-uwa mu tanadi wadannan domin jin
dadinmu da na mazajenmu da Kara gyara duk
wani kayan amfanin.

⊂( ̄ ̄)⊃ GIRKI MAI KYAU DA DADI ⊂( ̄ ̄)⊃

yake Yar-uwa duk Inda kike, ki kasance mai iya
girki, domin duk
 ① KYANKI
② KWALLIYARKI

in dai ba ki iya girki ba, to ba magana saboda
mai-gida ba zai dinga kawo abokansa gidansa
ba, saboda babu girki fita kunyar daga wurin ki.
Ki Sani, idan har ba ki iya girki ba, to ki nemi
mai koya miki ko kuma ki dinga siyan littafan
girki, ki koya ko kuma ki fita gari ki koya ,kuma ba sai lallai girki mai kashe kudi ba, ki Lura da yana yin cefanen da mai gida yake kawowa.

Sai kiyi abincin ki dai-dai da shi, kuma ki tsara
yayi dadi, ya kuma zama mai kayan kyan gani
da Ido, mai tsafta , saboda idan kin kawo ma
mai gida , ba zaiyi kyamar ci ba.

Sannan kuma abinci da akeci sau uku a Rana
ya kasance kinyi Wanda zai dace da lokacin da
kuma yanayin da ake ciki, sannan ki Lura da
zabin mai gida wato yanayin irin abincin da ki
ka ga ya fiso da safe da Rana da dare.

MU FARKA DAGA BARCI SABODA YANZU NE
MUKE CIN LOKACIN MU:

abinda yasa nace haka, shine idan ba ki tsiri
yin wadannan abubuwan da kuruciyar ki ba,
kuma tun wuri ba, to yaushe ne Zaki yi?
Ko-ko sai lokacin da tsufa ya kamaki Kai da
furfura?

Saboda haka tun yanzu ya kamata mu San
abinda muka taka, tun lokacin bai kure mana
ba, saboda yanzun ne muke cikin lokacin mu,
kuma idan kika fara daga yanzu shine zai wuce
har tsufa dan haka mu kula da wadannan ga
su nan duk sigogi ne da hanyar Kara rike
maigidanki:

[ SUTURAN DAYA KAMATA KI DINGA SAKAWA]

irin wadannan suturun kuwa sune:
➽ ATAMFA:
Riga da zani ko siket, amma kuma ba matsatsu
ba, saboda idan kika saka matsatsu ,wani zai
iya zuwa ya shigo, lokacin da ba ki zata ba, da
Rana kenan ko da safe:
➜ SHADDA
➜ LESS
➜ MATERIAL
Duk na sawan safe da Rana ne:

                     ✿ LOKACIN MAI-GIDA ✿

sai kuma Riga da wando
👗 English wears:
👚 body hock:

Amma su wadannan na kwalliyar
🎗 dare ne
Babu Wanda ya kamata ya gansu sai maigidanki kuma idan Zaki saka to ki tabbatar
kin saka matsasu.

Wanda duk Inda kika juya ki na taku a cikin
gidan, to sai ya ji sha'awarki.

👗
NIGHT GOWN:
ita wannan kin San irin tata shigar, wato rigar
barci ce
( SLEEPING DRESS) 👗
ita ma duk wanda Zaki sa, ki tabbatar mai
daukar hankali ne, kuma wacce zata Kara fito
miki da surar jikinki, don haka an fi son asa 'yar shara-shara kuma mai Kama gwiwa.

. 📡◞MIJI◟⌨

Ki kasance mai kula da hakkin mijinki, idan
kuma ba haka ba, to koda ki na masa wadannan abubuwan da na lissafo to fa zai
dinga Neman matan banza a waje, wanda ba'a
fata!

Amma kuma laifinki ne, tunda ba kya iya sauke
masa bukatarsa, domin sai kin zage dantse ki
kasance mai juriya , tun ba in Allah ya ba ki miji mai yawan bukata ba (HARIJ) to fa sai kin yi hakuri da sannu Zaki Saba.

Duk hakkin miji da ya hau kanki, wanda ki ka
San ya zama dole a gareki, ki sauke masa, to
dole ne ki ba shi hakkin sa, musamman wurin
kwanciya domin idan ya Fara Neman mata a
waje, sai kin fi kowa bakin ciki Ga yadda cuta suka yawaita, ya je ya dauko, ki ya shafe ki,sai a kula..

┗0┓❀❀┗0┓✿✿┗0┓❀❀┗0┓✿✿┗0┓

           ✜✜✜ BABBAR MATSALA ✜✜✜

wata babbar matsala itace:

                 ▣•••FARKO-AURE•••▣

sai kaga soyayya da kulawa ga mai-gida
kamar a cinye juna.

Amma kash!

Sai dai daga baya, da zarar mace ta Fara
samun yara, sai kuma labarin ya sha bamban.

A JUYAWA MAI-GIDA.

duk wata kulawa sai ta kau, sai wanda ya
zama dole.

Ita kullum hankalin ta yana wurin yaranta

➽ kuskure ne babba matan hausawa muke yi
Domin ai komai da muhallinsa, yara dai koda
yaushe Ku na tare, ba kuma cewa aka yi kada
ki kula da suba.

Amma yayin da mai-gida uban gayya ya dawo,
ya dace ya samu kulawar data dace.

Don hakan ma da wasu ke yi, yana sa mai-gida
ya fita harkaki, ya koma wajen matan banza.
Ko kuma ya je wajen Hira,sai kin yi barci , ya
dawo tunda ya San ko ya dawo da wurin, ba
wata kulawa zai samu a gunki ba.

To meye ribarki da Kai da kaya fa, duk mallakar wuya ne.

Ma'ana dake da yaran duk zamansa kuke yi
Sai a kula, matukar kina son kina son kaunar
mijinki.

           ⊂ (MAI TATTAUSAN LAFAZI). ⊃

duk macen da take tausasa harshenta, a duk
lokacin da zata yi ma mijinta magana, to wannan matan mutumcinta damba ne.

Namiji zai dinga gani, kuma duk mai wannan
tausan lafazin ta fi Kara shiga zuciyar mijinta.
Don kuwa idan kina yi masa, zai dinga jin
maganar har cikin kwakwalwar kansa, don
haka 'yan'uwa mata mu dinga Lura da yadda
zamu dinga yima mazajenmu maganar, saboda
wannan abune mai matukar muhimmanci a
zamantakewar aure, saboda suna bala'in
kaunar mai masu magana cikin taushin lafazi.

             JAN_HANKALIN_MAI-GIDA

Ki dinga amfani da kissa da kisisina irin namu
na mata domin Kara Jan hankalin mijinki zuwa
Gare ki ta hanyar.

🍲 girki mai kyau da dadi
👗 kananan kaya matsasu
✎ tsafta
👜 iya kwalliya
☛ gyaran gashi.

                 IYA KWANCIYA DA MIJI 

da salo-salo kwanciya iya karkada jiki da
girgiza kirji yadda hankalinsa zai rinka tashi
Da sauransu :

            ☆O☆•• SHAGWABA ••★O★

duk namiji yana mutuwar son mace mai
shagwaba, domin kuwa yana karasa ki Kara
tasiri a zuciyar mijinki, don haka 'Yar-uwa ki
Lura idan yana gida ki dinga kusanta kanki da
shi, ki na narkewa a jikinsa, ki na masa
shagwaba kamar karamar yarinya tare da dan
kuka-kukan shagwaba, yadda Zaki Kara shiga
zuciyarsa sosai.

Saboda duk abinda kika ce ki na so mijinki ba
zai dinga jin kyashin ba ki ba, kuma idan ma
yana miki wulakanci, Zaki ga ya daina insha
Allah, in dai kika yi amfani da shawarar Dana
bayar.

Saboda haka koda yaushe idan yana gida, ki
dinga makale masa, kada ki Bari Ku dinga yin
nisa da juna, koda yaushe ki dinga zabga
masa shagwaba, kina Kara narke masa a jiki
kamar mage, kuma ko magana Zaki yi da shi,
to ya kasance cikin sigar shagwaba Zaki dinga
yi masa...

^▽^MAGANIN TARI NA YARA DA MANYA MAI TSANANI^▽^

Tari mai tsanani abune da ke sanya mutum ya
gaji lokacin guda saboda yawan amfani da
energy da mutum ke yi lokacin tarin, yana iya
janyo ciwon Kai, ciwon kirji, yana Hana yin barci da sauransu.

Idan yaro ko babba na fama da wannan lalura
sai abi wadannan hanyoyin don magance
wannan lalura kamar haka.
➽ farar albasa
➽ zuma
A samu manyan farin albasa guda 2 a dafa shi
da ruwa kofi 2 bayan ya dahu sai a tsiyaye asa
zuma asa sake dafawa don ya yi kauri sai a
sauke a barshi yayi sanyi Ana shan cikin
cokalin bayan anci abinci har wata 2 wannan
babban mutum ma zai iya yi amma sai babban
cokali zai yi amfani da shi ba karamin ba.

Post a Comment

0 Comments