MAGANIN BASIR


◆☛ MAGANIN BASIR ☚◆

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

Idan basir yayi tsiro Ana samu danya, zait lauz, a kwaba shi da danyan kwal egg a dinga turawa a cikin dubura, yana kashe basir mai tsiro ,kuma yana konar da basir da yake toshe bakin dubura.

       ◆☛ CIWON BASIR ☚◆

a samu ganyen riyhan busasshe sai a daka shi yayi laushi sannan a samu man
zaitun ko habbatussauda sai a kwaba a rinka cusawa ta dubura.

Za a yi haka sau biyar a yini daya.

                 ☆▽ 2 ▽☆

A samu shibtu a rinka hadawa da Zuma ana sha a kuma rage kadan a rinka cusawa a dubura.

a dinga shan habbatussauda safe da yamma Ko zuma
man zaitun Suna magani basir.

3
A samu za'afaran a daka shi a hada shi da kwaduwar kwai egg danye a rinka sha safe
da yamma.

4
A samu wadannan mahadan
■ fulful
■ citta
■ tafarnuwa
■ gishiri

Sai a daka su waje daya a rinka dibar cokali daya ana hadawa da Zuma Ana sha sau daya safe da yamma.

da yawa mutane suna kasa banbancewa meye basir,da yawa mutum daga yaji cikinsa
yana kugi ko yana ciwo sai yace basir yanabdamunsa, amma da yawa wasu cututtu sunabkama da basir kuma yana cutarwa da yawa,byakan sa sha'awar mutum ta bangaren jima'I ta dauke, ya kansa ciwon ulcer dominbyana hana cin abinci, yana kuma kawo wata cuta wadda ake ce wa (sha'awatul kaziba),shine mutum daya fara cin abinci sai yaji ya koshi.

Kowa da kowa zai iya samun wannan matsala ta Basir, maza da mata.

Amma ba a cika ganinsa ga yara ba, an fi ganinsa ga manya, Kuma kowa zai iya
samunsa a kalla sau daya a rayuwarsa.

A manyan ma sai masu nauyi sosai, kamar mutane masu kiba.

A mata za a ga basir ya fi yawa a lokacin da mace ta samu juna biyu saboda nauyin da ta kara yayin daukar ciki, Idan ta haihu kuma ya baje.

A likitance basir shi ne ciwon jijiyoyi ko magudanan jini na dubura, na can ciki ko na waje-waje, wadanda suke kumbura su kuma yi ta ciwo.

Wasu abubuwan da ake gani su ke kawo wannan ciwo sun hada da;

☛ Yawan zama wuri daya na tsawon lokaci Yawan bayan gida mai tauri shi ma kan sa
jijiyoyi ko magudanan jinin dubura su kumbura su rika ciwo.

☛ A dukkan wadannan yanayi, magudanan jinin suna kumbura, su ja ruwa, wani lokaci su fashe.

☛ Shi ya sa mai basir wani lokaci ya kan ji zafi ko ciwo a dubura, wani lokacin ma har
da zubar jini.

☆ Basir Ya kasu kaahi uku, ☆

Akwai na cikin dubura da kuma na kasa,akwai kuma mai tsuro wanda akan ji shi
yana saukowa, har sai an mayar da shi.

HANYOYI KARIYA;

Hanyoyin sun hada da yawan motsa jiki da yawan hada ganyayyaki a cikin abinci da
yawan cin ’ya’yan itatuwa, Wadanda duka sukan sa bayan gida laushi.

MAGANINSA;

Anusol akansa wannann Magani a dubura in za a kwanta da dare, sai a hada da tsarki da ruwan zafi a buta wanda aka sa wa gishiri kwatankwacin cikin hannu daya.

Za'a iya atafasa sassaken mangwaro da zuma za'a warke in sha Allahu.

Za'a kuma iya samun sassaken Madaci a dafa asaka gishiri cikin cokali uku.

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

Post a Comment

0 Comments