Akwai wani mutum daya samu ɗaya daga cikin mashahuran malaman musulunci kuma mai hikima ya kai masa korafi kamar haka:
"A lokacin dana fara haɗuwa da matata ya kasance itace abu mafi soyuwa kuma mafi kyawu a idona daga dukkan halittun ubangiji"
Yaci gaba da cewa "A lokacin da muka fara soyayya har muke shirin aure, sai na fara ganin wasu matan waɗanda suka kaita a kyau" Bayan kuma na aureta sai nake ganin mafiya yawan mata sun fita kyau. Bayan mun ɗauki shekaru, sai nake ganin dukkan matan duniya sun fita kyau, aji da kuma birgewa"
Sai malamin ya ce "bana fada maka abinda yafi wannan ɗaci ba?
Sai mutumin yace "fadamin mana"
Malam: "Da ace zaka auri dukkan matan duniyan nan, toh da zaka ga kare wanda yake gararamba a titi sai kaji yafi birgeka akan su matan naka"
Mutumin: Meyasa kace haka malam?
Malam: "Saboda matsalar bata matarka bace, matukar mutum ya na da budurwar zuciya, kuma yana yawan kallace kallace toh babu abinda zai wadaceshi face kasar kabarinsa. Matsalarka itace baka rintse idanuwan ka daga kallon abinda Allah {S.W.A} Ya hana ka. Shin kana so kaga matarka kyakkyawa kamar yadda kake ganinta kafin ka aureta?
Mutumin: Eh inaso
Malam: Ka rintse ganinka saboda fadin Allah {S.W.A} "Kuma ka fada wa muminai maza su saukar da idanunsu ƙasa, kuma su kare al'aurarsu. Wannan shi yafi tsarki a garesu, kuma Allah shine mafi sani akan abinda suke aikatawa" Suratul Nur.
Hakika ya na da daga dabi'ar mutum: abinda ba nasa ba yafi ƙayatar dashi. Amma a lokacin daka samu abin sai kaga ya tashi daga something special to something ordinary
Ka kasance mai godiya da kuma wadatar zuci daga abinda Allah ya baka. Bin dokokin Allah shine abinda yafi alkhairi. Sannan ka dinga yawan addu'a akan Allah ya sanya ka dinga ganin kyanta. Ya sa kuma ka kaunaceta da kuma tausaya mata a koyaushe"
Annabi {S.A.W} yana cewa "Idan ɗayanku yaga wata mace data birgeshi, toh ya koma gida ga matarsa domin abinda ta wajen take dashi, itama matarsa tana dashi"
Ya Allah ka ƙara tsare mana imanin mu.
Gabatarwa :-
0 Comments