Daga Dr Auwal Ahmed Musa
A lokacin watan Ramadan wasu na wahala sosai saboda wasu abubuwa da suke aikatawa ko kuma wasu abinci da suke ci.
Idan ka na son kayi azumi a SAUKAKE, toh ka aikata abubuwa kamar haka:
1. Cin sahur.
Cin abinci ko abin sha da ya kamata yana taimakawa domin rage wahala ko gajiya a lokacin azumi.
A duk lokacin da mutum bai yi sahur ba, zai kasance babu abinci a cikin jinin sa saboda haka zai ji yunwa kuma zai iya wahala.
Rashin cin sahur na iya saka jin kishin ruwa da gajiya. Kuma zai kasance mutum ya yi azumi awoyi fiye da sauran Musulmi.
2. Kada ka cika ciki ya wice wuri a lokacin buɗe baki.
Idan ka cika ciki fiye da kima cikin ka na iya lalacewa kuma yana i saka ka kiba mai yawa.
3. Ka rake cin maiko dayawa ko gishiri da yawa ko zaki/ sugar
Maiko mai yawa na tada olsa. Yawan gishiri na iya saka mutum yawan fitsari. Haka sugar ko zaki na saka yawan yin fitsari kuma yawan fitsari na sa yawan jin kishi ruwa tare da wahala a lokacin azumi.
4. Ka yawaita shan ruwa a lokacin sahur da bayan buɗe baki.
Shan ruwa sosai a lokacin sahur na iya rage wahala da ragewar ruwa a jiki a lokacin azumi.
Hakan zai sa a yi azumi a saukake.
5. Yawaita cin ganye da shan kayan lambu/ gona.
Wannan yana kara lafiya da garkuwar jiki tare da bada ikon yin azumi a saukake.
6. Daina shan lipton ko nescafe a lokacin sahur. Shan lipton ko nescafe a lokacin sahur na sa yawan fitsari da ragewar ruwa a jiki da tada olsa. Hakan na iya sa mutum ya wahala sosai.
Allah Ya sa mu dace.
Allah Ya karbi ibadun mu.
Ameen.
0 Comments