GUZURIN MASU CIKI


🤰🏽 GUZURIN MASU CIKI 🤰🏽 :

>>>>>>>>>>>>
🤰🏽🤰🏽🤰🏽
Sirrinrikemiji@gmail.com
Sirinrikemiji@gmail.com
☏+2348037538596

Abinda gangar jikinta yake bukata sune kamar haka :

🤰🏽 Hutu tare da kwancyar hankali.

🤰🏽 Ta yawaita cin ganye (Kayan lambu) da kuma 'Ya'yan itace.

🤰🏽 Ta rika motsa jiki lokaci lokaci domin jinin jikinta ya rika zagawa sosai.

🤰🏽 Ta rika shan shayin ganyen Na'a-Na'a domin samar da Qarfin jiki da kuma Kaifin basira ga jaririnta.

🤰🏽 Ta rika amfani da Zuma domin samar da kuzari da kuma riga-kafi gareta da kuma jaririnta daga chututtuka.

🤰🏽 Idan lokacin haihuwarta ya kusanto ta nemi dabino danye nunanne (irin wanda ake kira Siki) ta rika yawan cinsa. Idan bata sameshi ba, oda busashen ne ta rika amfani dashi.

🤰🏽 Shan dafaffiyar garin hulba shima yakan yi amfani ga masu tsohon ciki. Yakan bama mahaifar Mace karfin turowa jaririn idan lokacin fitarsa yayi.

Ki rika shafa Man Tafarnuwa ko man Jirjir ko man Habbatus sauda domin magance ciwon Qafa din.

 Wadannan duk ba zasu chutar da mai ciki ba. Koda shansu akayi.


*🤰🏽 SADUWA DA MAI CIKI🤰🏽*
Sirrinrikemiji@gmail.com
Sirinrikemiji@gmail.com
☏+2348037538596

 ya halatta a sadu damace lokacin da take da ciki, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa"

 Abu-dawud : 1847 Ibnul kayim yana cewa :"Wannan hadisi yana nuna cewa ciki yana kara karfi duk lokacin da ake saduwa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kamanta shi da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka ba ta ruwa"

 Tahzibussunan 1\193 . Masana likitanci suna cewa: Ba'a so miji ya dinga hawa kan matarsa lokacin da take da ciki, zai fi kyau ta dinga yin goho yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe, saboda kwanciya akanta yana iya wahalar da yaron . Sannan yawanci mata ba su cika son yawan saduwa ba idan cikinsu ya girma, wasu likitocin suna bada shawara cewa a karanta saduwa a wadannan lokutan. Allah ne ma fi sani .

Post a Comment

0 Comments