Sirrinrikemiji@gmail.com
Sirinrikemiji@gmail.com
☏+2348037538596
‘Hips’
'Girmam Kugu'
Girman kugun mace yana daya daga cikin
abubuwan dake janyo sha'awa tare da tayar da
hankalin maigida idan ya kalli uwar-gida
musamman idan tayi kwaliyya da matsatsun
kaya masu nuna shape din jikinta.
Shidai 'Hips' a jikin mace wata baiwa ce ta
halitta wacce Allah yakan halici dan Adam da ita, Wadansu matan suna matukar sha'awan su kasance masu cikan 'Hips' Amman Allah bai basu ba.
Hakan yasa na kalato ma irin wadannan matan
hanyoyin da yafi dacewa su bi wajen samun
cikar 'Hips' batare da samun illoli a jikinsu ba.
Wasu matan har kauce hanya suke yi, su je a
saka musu 'Hips' din roba.
Kun ga akwai alamar kauce Hanya a nan ke nan.
Akwai nau’in ababen da mace za ta rika ci,
sannu a hankali, kyan diri da halittarta za su kara fitowa,ita ma za ta rika ji ta kara cika, ta yi kyau.
Masana a wannan fannin, sun bayar da
shawarwarin amfani da Abarba, Ayaba, Gwanda,
Kankana, Zuma, Madarar ruwa. A kan hada su
waje guda, a markada su, har sai sun zama ruwa, sai a dan kara zuma da madara. Bayan wannan, mace za ta rika sha a koda yaushe.
Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe, ki
hada da ganyen Alayahu, ki zuba Tumatiri da Albasa,ki yi kwadonsu, ki rika ci. Haka nan za ki rika yin wadannan kayan lambun da ki ka markada, sai ki rika sha misali da asuba ko da sassafe kafin ki fara cin komai.
Insha Allah za a dace.
GODIYA TA MUSAMMAN :
ga masoya wannan shafi sirrin rike miji.
☏+2348037538596
sirrinrikemiji@gmail.com
Sirinrikemiji@gmail.com
0 Comments