Ina takaici na ga ana azumi amman wasu na zage-zage ga junansu a Facebook, wasu kuma labaran karya suke yadawa, wasu kuma su kirkiri labarin karya ko su yada don nishadantar da mutane, hakika duk masu aikata haka suna aikata babban kuskure, Annabi S.A.W yace" Allah baya bukatar yunwarsu da kishirwarsu,"
Kamar yadda Bukhari ya kawo Hadisin a cikin Sahihinsa Manzon Allah S.A.W yace,"
ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺁﺩﻡ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺇﻳﺎﺱ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺫﺋﺐ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺳﻌﻴﺪ ﺍﻟﻤﻘﺒﺮﻱ ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﻣﻦ ﻟﻢ ﻳﺪﻉ ﻗﻮﻝ ﺍﻟﺰﻭﺭ ﻭﺍﻟﻌﻤﻞ ﺑﻪ ﻓﻠﻴﺲ ﻟﻠﻪ ﺣﺎﺟﺔ ﻓﻲ ﺃﻥ ﻳﺪﻉ ﻃﻌﺎﻣﻪ ﻭﺷﺮﺍﺑﻪ
Annabi yace" Duk wanda be bar fadin karya da aiki da ita ba, to Allah baya butakar daina cin Abincinsa da shan ruwansa"
Sannan za ka ga mutum da Azumi a bakinsa amman sai yazo Facebook yana Comment yana dura ashariya yana zagin mutane, abun takaici maimakon wanda aka zaga ya hakura shima sai ka ga yayi zagi da niyyar ramuwa, to da wanda ya fara zagin da wanda ya rama zagin duk sun bar koyarwar Annabi, yazo a Bukhari 1894, Manzon Allah S.A.W yace"
ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﺴﻠﻤﺔ ﻋﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﺰﻧﺎﺩ ﻋﻦ ﺍﻷﻋﺮﺝ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ: ﺍﻟﺼﻴﺎﻡ ﺟﻨﺔ، ﻓﻼ ﻳﺮﻓﺚ ﻭﻻ ﻳﺠﻬﻞ، ﻭﺇﻥ ﺍﻣﺮﺅ ﻗﺎﺗﻠﻪ ﺃﻭ ﺷﺎﺗﻤﻪ ﻓﻠﻴﻘﻞ ﺇﻧﻲ ﺻﺎﺋﻢ. ﻣﺮﺗﻴﻦ، ﻭﺍﻟﺬﻱ ﻧﻔﺴﻲ ﺑﻴﺪﻩ ﻟﺨﻠﻮﻑ ﻓﻢ ﺍﻟﺼﺎﺋﻢ ﺃﻃﻴﺐ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻣﻦ ﺭﻳﺢ ﺍﻟﻤﺴﻚ، ﻳﺘﺮﻙ ﻃﻌﺎﻣﻪ ﻭﺷﺮﺍﺑﻪ ﻭﺷﻬﻮﺗﻪ ﻣﻦ ﺃﺟﻠﻲ، ﺍﻟﺼﻴﺎﻡ ﻟﻲ، ﻭﺃﻧﺎ ﺃﺟﺰﻱ ﺑﻪ، ﻭﺍﻟﺤﺴﻨﺔ ﺑﻌﺸﺮ ﺃﻣﺜﺎﻟﻬﺎ
Annabi yace" Azumi Garkuwa ne, wanda yake Azumi ka da yayi kwarkwasa ko wani Abin Allah wadai, ko Abin Jahilci, Idan wani ya nemi ya yi fada da shi ko wani ya zage shi, to Yace NI MAI AZUMI NE, NI MAI AZUMI NE, Manzon Rahma yaci gaba da da cewa" na rantse da wanda raina yake hannunsa, hamamin bakin me azumi yafi dadi a wajen Allah fiye da turaren almiski, me Azumi yana Barin ci da sha da Sha'awarsa saboda ni. Azumi nawa ne, kuma zan sakamako da shi, kowacce kyakkyawa guda daya da goma na misalinta. Karshen Hadisin yazo da Siga irin ta Hadisul kudsi, Wanda tana komawa zuwa ga Allah S.W.A
Idan muka duba wadannan Hadisai, yakai 'dan uwa karya ba taka bace, haka copy da paste na labarin karya shi ma ba naka bane, fada ba naka bane koda kaine me gaskiya, haka koda wani ne ya zageka duk yadda ka kai ga fusata kada ka biye masa, ka yi Amfani da Fadin Annabi S.A.W
Allah ka karbi ibadarmu kasa muna cikin 'yantattu.
Indabawa Aliyu Imam
0 Comments