๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป
Kamar yadda na amsa wata tambaya akan ko ya dace mai ciki tasha ruwan sanyi! Eh normal ne babu matsala. Shan ruwan sanyi shi akaran kansa baida matsala ko illa ajika ga lafiyayyen mutum.
Eh Ba matsala ga lafiyayyen mutum nace! Mutum wanda ruwan baya basa allegic reaction na tari ko mura duk sanda yasha, wanda kuma baida ciwon hakori ko saurin cuttuka na cikin baki. Kurum mutum ne de da ko yasha ba abunda yakeji dama kurum de yanaso yasani ne ko akwai wata matsala agaba ko babu kan hakan.
Saide tunda batu ake na azumi akwai wasu lokuta na daban da ba'a cika so asha ba:
■ Ba'a son asha ruwan sanyi karara ko ruwan kankara a lokacin da ake ajiye azumi wato shan ruwa (Iftar) bayan ankira sallar magariba. Dalilin shine ka keto awoyi masiu yawa batare da ci ko shan komi ba, hakan yasa duk kayan cikinka atakure suke, sun galabaita sun dau zafi sun fata kona kansu da kansu domin baka kuzari... don haka shan ruwan sanyin zaisa jijiyoyin jini su motse wanda hakan musamman in ansha ruwan sosai ka iya haddasawa mutum murdewar ciki, tashin zuciya, amai da cushewar ciki.
■ Haka ba'a son shan ruwan sanyi bayan gama cin abinci, ko kuwa tsakiyar cun abinci, musamman abinci me maiko saboda hakan na qara sanya kasala da rashin karsashi ga sassan sarrafa abincin... tunda dama digeestion aikin parasympathetic nervous system yana faruwa ne AT REST, toh cigaba da tafka ruwan sanyi acikin na iya jawo mutum ya rika haduwa da 6acin ciki in abun ya zamo hali koda ba lokacin azumi ba. Nan da nan tdakiyar cin abinci kaji ka tashi ka ruga bandaki kana sakin gudawa fata-fataa tsuuuu
■ Ba'a son shan ruwan sanyi a lokacin da aka gama motsa jiki wato workout ko guje-gujen kwallon kafa. Saboda already ta cikinka kai generating heat don haka kamar yadda bazakai wanka da ruwan sanyi cikin halin zufa ba haka ma shansa aciki.
Wadancan lokuta guda uku sune akeson adaga masa kafa koda za'a asha afara da mara sanyi karara ko me dumi kafin daga bisani bayan mintuna 3 zuwa 5 sai a biyo bayansa dame sanyin koda kuwa lemon juice ne.
๐๐บ๐บ๐ฎ ๐๐ฎ๐ป๐ฑ๐ฎ ๐ธ๐ฎ ๐ฎ๐ท๐ฒ ๐ฎ๐๐๐บ๐ถ๐ป:
Right away! zaka iya shan me dan sanyi-sanyi wato ruwa wanda yake bana fridge ba. In kanason fahimtar wanda ya dace da jikinka a lokacin ka auna sanyin da muhallin (daki/shagon) da kake zaune daidai sanyin daki ko rumfar da kake zaune daidai sanyin ruwan da jikinka ke bukata kenan.....
Don haka idan tempreture din gurin me dumi ce toh jikinka irin ruwan da yake bukata kenan a wannan lokacin, inkuma cikin na'urar Ac kake toh nan ma haka! Wannan itace hanya ce mafi sauki kurum.
Amma de karku manta shawara ce! Tunda duk da hakan wasu suna da karfin metabolism sosai, ko sunsha basajin komi, sannan wasu shan nasu chance ne bawai kullum bane suke samun hakan,
Amma in mutum nada wasu larurori ko kuwa yasan inyasha yana samun matsala toh ya hakura, kamar masu ciwon Asthma hakan na iya tada ita wa wasu, Haka masu matsanancin ciwon 6arin kai guda irin na gado wato Migraine ruwan sanyi ma yana iya tashinsa, kode duk wata cuta me alaka da numfashi.
Sannan in akwai dadaddiyar ulcer wacce bata samu kulawa ba saboda azumin da akayo shan ruwa me sanyin gaske na iya sa mutum tashin zuciya wanda yana iya kaiwa ga amai koma ulcer din ta tashi saboda ai gyambo ce, gyambo ko kowanda yake akafa inba kulawa ya kanyi wari aji, ballantana na cikin ciki da baya samun iska sai anbude baki.
Don haka su wadancan matsaloli duk ba dole ka fuskancesu ba alokaci daya ko lokacin da kasha.
๐ฆ๐ฎ๐ถ๐ฑ๐ฒ:
Shan luke-warm wato ruwan dumi be zafi can ba, ko wanda yai daidai da yanayin gurin da kake wannan shi yafi dacewa da jiki kuma shike taimakawa jikin wajen saurin sarrafawa tare da narkar da abinci da karawa sashin sarrafa abinci inganci...
Kiyaye hakan kesa wasu insun kai azumin kaga sun iya cin abinci sosai, amma wanda yaita dirkar ruwan sanyi shine zakaji yana yama kasa cin abincin ko kuwa daga cin kadan shikenan... saboda ya kashe kuzarin kayan cikinsa.
Don haka ga wanda yakai azumi in son samu ne ya sami ruwan dumi ko lukewarm yasha bayan kamar minti 10 zuwa 15 sai yabi dana sanyin da yakeso hakan shine yafi inma ya zama dole sai ansha kenan.
Amma de kai tsaye bawani sananniyar illah ga shan ruwan sanyi sama da rage karsashin kayan ciki ko jawo tashin zuciya.
✍๐ผ
[๐ฐ๐๐๐๐๐๐ ๐. ๐๐๐๐๐]
0 Comments