Idan aka ce Ewedu wani ganye ne mai yauqi wanda ake yin miya da shi, da hausa ana Kiransa da sunaye kamar haka: *AYAYO, LALO ko kuma MULUHIYA*.
Ga kadan daga cikin amfaninsa a jikin mu kamar haka:
1- Yana karawa idanuwa lafiya .
2- Yana samar da sinadarin da ke hana kamuwa da cutar Cancer (Daaji).
3- Yana karawa gashi lafiya.
4- Yana baiwa haƙora/haure kariya daga kamuwa da cututtuka.
5- Yana kiyaye lafiyar fata.
6- Yana fitar da sugar da take cikin jini.
7- Yana karfafar mazantakar namiji, Kuma ya karfafa masa gabobinsa.
8- Yana samar da sinadaran da mace mai ciki ke bukata wajan kwarin kasusuwan ta da kwarin jikinta.
YADDA AKE YIN MIYAR EWEDU DON DACEWA DA WANNAN AMFANIN:
1- Ba a dafa shi ya dahu sosai kamar yadda yawancin al'ummar hausa/Fulani keyi, kuma anfi so a dafa shi shi kadai ( ba dafa-duka ba) kuma a sanya daudawa/daddawa sosai aciki sai ayi masa miyar stew ko dage-dagensa dabam.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
0 Comments