Amfanin kubewa guda 12 a jikin Dan Adam:






Kubuwa wata nauyin kayan lambu ne da akan yi amfani wajen yin miya. Hasashe sun nuna cewar Kubewa ta samo asali ne daga kasar Habasha wato Ethiopia da kuma Masar wato Egypt tun karni na 12.


Mutane da dama na shan miyar kubewa don dandano da dadinta ne kawai ba tare da sanin tarin alfanun da ke tattare da ita ba.

Hakan yasa muka binciko maku kadan daga cikin amfaninta a matsayin magani ga garkuwar jikin Dan Adam.


Ga su nan kamar haka:

1. Ana amfani da kubewa wajen maganin cutar siga wacce ta zamo ruwan dare a tsakanin al'umma a yanzu. Tana dauke da sinadarin fibre a cikinta, wanda ke taimakawa wajen daidaita yawan siga a cikin jikin dan Adam, wanda kuma ke rage karfi ciwon siga ko ma maganinsa.

2. Kubewa na matukar tallafa wa masu juna biyu wajen inganta lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki domin kubewa na kunshe da dimbin Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki da. lafiyarsa.


3. Ta na kuma maganin cutar wahala wajen fitar da numfashi wato Asthma, saboda sinadarin Vitamin C da ke tattare ta ita.


4. Ga mai son kara inganta fatan jikin sa ya yi laushi da santsi kamar yaukin kubewar toh ya lazumci amfani da ita.

5. Yana matukar maganin karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai. Kuma yawan amfani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har ya yi wa mutum lahani ba.



6. Masu ciki kan iya amfani da kubewa domin ingancin lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki domin kubewa na kunshe da dimbin Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki (cells) da kuma ( folates) don haka kubewa na hana haihuwar jariri mai dauke da wasu nakasu a jikinsa kuma na sa jaririn ya girma a ciki kuma da koshin lafiya yadda ake so. 

Haka kuma jaririn da ke ciki zai iya amfana da dimbin Vitamin C dake cikin kubewa domin kare lafiyarsa.

7. Kubewa na maganin ciwon koda. Wani bincike daga jami?ar Jilin ta kasar Sin ya tabbatar da wannan. Binciken. Ya nuna cewar wadanda suke ci ko shan kubewa a kullun sun nuna nasarar rashin lalacewar koda musamman wadanda ke da ciwon sugar domin kusan kasha 50 na masu matsalar koda sun samu matsalar ne saboda suna da ciwon sugar.

8. Kubewa na kara lafiyar dubura (colon) wato karshen babban hanji.yana wanke hanji da tumbi sosai don haka yana maganin kumburin ciki. 

Kuma Vitamin A da ke cikin kubewa na taimakawa lafiyar wani abu kamar majina (Mucous membranes) na cikin babban hanji.

9. Kubewa na maganin Asthma da wasu cututtukan numfashi. Yana dauke da Vitamin C da ke taimakawa hanyoyin numfashi.

10. Kubewa na kara ingancin fatan jikin mutum yay i laushi da santsi kamar yaukin kubewa. Ka ga mutum kullun kamar yaro ko yarinya a fatarsa.

Yana kuma taimakawa wajen mayar da fatar da ta lalace (Meosis).

11. Yana matukar maganin Anaemia wato karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai. Kuma yawan amfaani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har yayi maka lahani ba (blood coagulation).

12. Yawan sha ko cin kubewa na matukar rage nauyin jiki ga wadanda suke jin kiba ya musu yawa.

Post a Comment

0 Comments