Amfanin "Dauɗar Kunne" Da Illar Ƙwaƙwale Ta.




"Dauɗar kunne" wani ruwa ne mai ɗan danƙo da dodon kunne ke samarwa domin bai wa kunne kariya, saɓanin yadda Bahaushe ke cewa "dauɗar kunne" ce . Saboda haka "dauɗar kunne" ba dauɗar kazanta ba ce, face wata hanya ce da kunne ke samar wa kansa kariya daga baƙin abubuwa da ka iya shigowa daga waje. 

Allah da ikonsa, kamar yadda kunne ne ke samar da wannan "dauɗar kunne", haka nan kunnen ke da ikon yashe wannan "dauɗa" da kansa.

Daga cikin amfanin "dauɗar kunne" akwai:

1. Cafke dukkan nau'in ƙura, ƙasa, ƙwari ko yayi kafin su kai ga cikin kunne.

2. Kashe kwayoyin bakteriya, da sauransu.

Saboda haka kada ka yi amfani da waɗannan abubuwa don ƙwaƙwale dauɗar kunne:

1. Magogin kunne wato 'cotton bud' a turance.

2. Tsinken tsintsiya

3. Mirfin biro

4. Kan ashana

5. Gashin kaza, da makamantansu.

Sanya waɗannan abubuwa cikin kunne don ƙwaƙwalo "dauɗar kunne" na da haɗarin:

1. Ƙara cusa "dauɗar" zuwa can cikin kunne.

2. Kareraya gasun cikin kwararon kunne, wanda suke amfani wajen kare kunne daga baƙin abubuwa daga waje.

3. Cusa irin waɗannan abubuwa na da haɗarin shigar da ƙwayoyin cuta cikin kunne.

4. Raunata gangan kunne yayin da irin waɗannan abubuwa suka zarme cikin kunne.

5. Shafe ko manne "dauɗar kunnen" a kwararon kunne.

Haka nan, zira waɗannan abubuwa cikin kunne don susa ko ƙwaƙwalo "dauɗar" akai-akai zai share kwararon kunne, kuma share ƙwararon kunnen na nufin share kariyar da Allah ya shirya wa kunne. Saboda haka, dukkan baƙin abubuwa na iya kutsa kai cikin kunne kai tsaye.

Kada ka ɗauki ɗabi'ar sa magogin kunne cikin kunne don goge "dauɗar kunne" kullum. 

Tuntuɓi likitan kunne da zarar ka fara jin wani ɓaƙon yanayi a kunnenka, ko neman shawarwari kan tsabtace kunne daga "dauɗar kunnen".

#Ear_Wax
#Ceruminosis
#Otitis_Media

Post a Comment

0 Comments