Hanyoyin kara tsawon gashi...
☏+2348037538596
✎ sirrin rike miji
Mata da yawa na son ganin gashinsu ya kara tsawo, hakan ba zai samu ba har sai sun rika kula da gashinsu, kasancewar gashi na kara wa mace kyau. Akwai hanyoyi da dama wadanda muka kawo miki a yau, idan kika bi su sau da kafa za su taimaka miki wajen kara wa gashinki tsawo, baki da yalki da kuma karfi. Wani abu dangane da wadannan hanyoyin shi ne, ba sa bukatar ki kashe kudi.
· Daga farko ki dora man kwakwa a wuta sannan sai ki zuba masa man amla. Daga nan sai ki gauraya sosai, idan kin tabbata sun gaurayu, sai ki sauke daga wuta, har hadin ya huce. Sai ki zuba man a kwalba ko murta. Kina shafa wannan hadin a fatar kanki da gashinki kamar sau uku a sati..
· Lemun tsami na sanya tsawon gashi sosai. Ki samu ruwan lemun tsami, sai ki hada shi da kwai da kuma man amla. Sai ki shafa hadin a fatar kai da kuma gashi. Ki bar hadin a kanki har tsawon minti 30, sannan ki wanke da ruwan dumi. Za ki iya yin wannan hadin sau 2 a wata.
· Ki samu ruwan Aloe bera, sai ki shafa a fatar kai da kuma gashi, bayan minti 20 sai ki wanke da ruwan dumi.
· Man zaitun na sanya gashi ya yi baki, taushi da kuma tsawo. Za ki iya mayar da man zaitun ya zama man kitsonki.
Muna so ku san cewa za ku iya zabar daya daga cikin wadannan hanyoyin, domin kowace hanya za ta biya miki bukata. Idan kuwa kika yi amfani da gaba dayansu, za su iya sanya a garin gyaran gira ki rasa ido.
☏+2348037538596
✎ sirrin rike miji
Hanyoyi goma wanda za a bi don gyaran jiki...
☏+2348037538596
● Idan ana so a gyara gashi za a iya hada ayaba da dwai sai a kwaba su sosai sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar zuwa talatin sannan a wanke.
● domin gyaran farce, za a iya tsoma hannu a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar sannan sai a cire a kullum. Farce zai yi kyau sosai.
● Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai sulbi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar zuwa ashirin sannan a wanke da ruwan dumi. A gwada wannan hadin sau daya a sati za a ga canji.
● Ana amfani da ruwan amfuna da ruwa ana wanke kai. Yin hakan na cire dattin da ke madale a gefen gashin kai.
● Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rida shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka badin da ya bayyana a wasu gafen fata.
● Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaba sai a rida dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.
● Man kwa-kwa na matudar gyaran zubewar gashin ka. Za a iya shafa man kwa-kwa a fatar ka, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa daya sannan a wanke.
● Maza masu son man gyaran gemu, za su iya amfani da man kwa-kwa.
● A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai.Sannan a rida shafawa a kan durajen fuska. Yin hakan na kasha su sosai.
● Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata.
(⌒MAHADIN GYRAN GASHI⌒)
☏+2348037538596
wannan hadi zai tai makawa mace wadda
gashin ta yake yawan lalacewa, domin kuwa
gashinki ba shi ba karai rayewa zai rinka laushi
kuma ya Kara tsaho idan har kina San kada ya
lalace kina iya samun wannan kiyi amfani dashi.
¹ ganyen Kai da magarya.
Ki da kashi kina yin amfani dashi wajan wanke
kanki wanke gashi da shi, yana kara karfafa gashi ya kuma hanashi zubewa ko kuma ki nemi:
¹ danyen kwai 2
² sabulun salo 3
³ garin shanmar.
A fasa kwai amma banda kwan duwar farin kadai Zaki yi amfani da shi, sai ki zuba sabulun salo a ciki, ki matse ki zuba garin shammar a ciki sai ki wanke Kai da shi idan har kina yin wannan hadin lai-lai kanki zai yi gashi mai kyau insha Allah.
● islamic medical center
0 Comments