GYARAN JIKINKI IDAN KIN HAIHU

✯・・☐▻FAMILY PLANNING ☐▻・・✯
♜ S・R・M islamic medical center ♜
⚑ sirrin ▻ rike ▻ miji ⚑
✁www.sirrinrikemijinki@yahoo.com
✁www.Sirrinrikemiji@gmail.com
∩↱D3C13938
⇢ whatsApp
☬+2348037538596

◇◇◇◇
◇◇◇
◇◇

GARE KU 'YAN MATA DA MATAN AURE DA SAMARI.YAKAMATA KUSAN
WANNAN DOMIN ZAI AMFANE KU..
.
Wannan saqon ya kunshi:
★Dalilin da ke jawowa 'yan mata yawan ciwon ciki ko mara musamman
bayan Haila
.
★Yanda ma'aurata zasu yi 'family planning' ba tareda shan magani ba.
.
★Abinda ke fitowa wasu mata mai kamar majina, dss.
Da farko, zan yi amfani da kalmomin hausa domin samun sauqin fahimta,
kalmomin turancin da ban san ma'anar su da hausa ba zan yi kwatancen da
za'a gane.
.
Idan nazo kan 'family planning zan yi bayani akan abinda bincike ya
tabbatar, amma ba sai na maimaita ba, Allah Ya kan iya canja ikonSa koda
anyi hakan kuma a samu haihuwa, amma Insha Allah ba'a cika samun
haihuwa ba idan akayi hakan.

A jikin mahaifar mace,(female reproductive system) idan kuka lura, zaku
ga wasu abubuwa kamar hannu guda biyu, daya gefen dama dayan kuma
gefen hagun, a bakin ko wanne akwai wani abu qullutu wanda a cikin sa
akwai wasu Qoyaye.

Duk sanda Mace tayi Jinin ta na Haila, bayan Jinin ya dauke da kwanaki 14,
wancan abu da muka ambata yana sake wadancan qoyayen, wadanda sune
sinadarin da ake hadawa a samu da.
Wadannan qoyaye idan aka sake su sukan shiga cikin mahaifar mace suyi
kwanaki 2 (48 hours) daga nan idan babu abinda yazo ya tava su (maniyin
Namiji) to zasu mutu.

Kafin a sake wadannan qoyayen akwai abinda Allah Ya halitta a cikin
mahaifar mace wanda zai zo ya share mahaifar ta sosai, domin mahaifar
zatayi baqo, wanda shine qoyin kenan..

Akwai wasu jijiyoyi guda biyu na jini, a gefen dama da hagu na mahaifar
mace, idan akazo aka share mahaifar, to wadannan jijiyoyin zasu cika da
jini sosai, sai su koma ja-ja-wur, suna jiran wannan baqon da zai shigo
mahaifa idan ya girma bai mutu ba sai suke bashi jinin nan a matsayin
abinci.

Maniyyin da Namiji yana yin kwanaki 3 (72 hours) a cikin mahaifar mace
kafin ya mutu.

✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯
Idan mun fahimci wadancan bayanan, to yanzu sai mu hada su waje daya
muga yadda abin yake.

Idan Mace ta gama haila da kwanaki 14 to wancan abh kamar tiyo na jikin
mahaifar ta yakan sake wadannan qoyayen, zasu shigo cikin mahaifar ta
suna jiran Maniyyin Namiji yazo ya same su, idan suka hadu, kuma komin
qarancin Maniyyin nan, to Maniyyin zai zamo musu kamar taki don haka
zasu hadu su girma, da hakane kuma Allah zai yita sallafa shi har ya maida shi mutum.

To idan babu wani Maniyyi da ya shigo gurin adalilin rashin saduwa da mace, to wadannan qoyayen zasu mutu bayan sunyi aha 48 (kwanaki 2), idan kuma suka mutu to zasu biyo cikin al'aurar mace sai su fito, sai kaji Mata na tambayar sukan ga wani abu mai kamar majina majina yana fito musu a al'aura, wannan shine abinda ke fitowar, wannan ya sa Malamai
suka ce babu komai akan wannan kawai ta wanke shi ba shida wani hukunci.

Adalin rashin shigar Maniyyi da zai girmar da wancan qoyi, sai wadancan jijiyoyi da suka tara jini a cikin su, sai suyi wani abu da ake qira fushi, basu ji dadi ba, adalin haka sai suke kartar jikin mahaifar mace, sai kaji mace
tace maka tana yawan fama da ciwon mara musamman idan ta gama Haila.

Anan zamu fahimci rashin aure ke jawo wannan, kuma maganin haka shine aure ko tiyata.

Idan karce jijiyoyin nan yayi yawa kuma aka yi rashin sa'a sai su fashe, idan kuma suka fashe zai jini yayita fita ba tsayawa, wannan shine ake qira da jinin Istihada, daman Manzon Allah (s.a.w) ya gayawa wata mata cewar ai wannan jinin jijiya ne.

Idan Matar aure ce kuma tana son yin 'family planning' da Mijinta, to hanya mafi sauqi itace; kamar yadda muka ji bayan gama hailar ta da kwanaki 14 ake sake wadancan qoyaye, kuma sukan yi kwanaki 2 kafim su mutu, shi
kuma Maniyyi yakan yi kwanaki 3 kafin ya mutu, to su ma'auratan kada su sadu tun ranar 12 da gama hailar ta, har sai bayan ranar 16 da gama hailar ta.

Ki dan tsaya kadan anan kafin ki cigaba kiyi tunanin meyasa akace haka? Dalilin hakan kuwa shine, ranar 14 qoyi ke zuwa, to idan suka sadu ranar 12, kada mu manta Maniyyi sai yayi kwanaki 3 kafin ya mutu, to kunga idan suka sadu ranar 12, maniyyin nan yananan a mahaifar yana jiran a sake qoyin, zai zauna na tsawon kwanaki 12,13,14 kafin ya mutu, to kunga zasu ci karo ranar 14, kuma babu abinda zai hanashi sarrafa qoyin nan.

Ance har sai bayan ranar 16 ne saboda shi kuma qoyi yakan yi kwanaki 2 kafin ya mutu.

To wadannan kwanaki 5 din-12,13,14,15,16 da gama Hailar mace, su ake qira da 'danger periods' ma'ana kwanaki masu hatsari, an qira su da hakane saboda idan dai aka sadu da Mace a wadannan kwanakin to kuwa tabbas
zata samu ciki, sai dai idan Mulkin Ubangiji ya shigo ciki, kuma idan ma'aurata na son yin 'family planning' wadannan kwanakin zasu kauce wa saduwa, ba sai sun sha magani ba, sai dai idan Mulkin Ubangiji ya shigo ciki.

❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖
FAMILY PLANNING ( 2 )

❀・ Yadda Ake Tazarar
Haihuwa・❀

Bisa ga tambayoyi da wannan fili ke yawan samu na hanyoyin tsara iyali, a yau za mu duba wannan mas’ala, domin ba kowa ba ne ya yarda a al’adarmu da addininmu cewa tsara iyali na da kyau ko ba shi da shi ba, amma dai domin amfanin masu karatu, da ilmin likitanci akwai lokutan da tsarin ke da amfani matuka gaya.
Da yake matan yanzu ba irin na da ba ne
saboda kujuba-kujubar rayuwa, yawanci matan sun fi son samun doguwar tazara kafin wata haihuwar.

Wasu kuma cewa suke matan na yanzu
ragwaye ne.

Akwai hanyoyin ba da tazarar haihuwa da dama. Duk kusan sun fi shafar
uwargida.

Hanyoyin da suka shafi uwar gida yawanci na asibiti ne, kamar allurai da kwayoyi da saka sinadarai daban-daban a mahaifa. Kuma
dukkansu suna da ’yan matsaloli wadanda suka hada da rikicewar al’ada ko ciwon mara ko kiba da dai sauran ire-irensu. Wadannan ’yan matsaloli sun bambanta daga wata mace zuwa wata. Wata ciwon mara kawai za ta yi,
wata kuma kiba kawai za ta yi, da kuma abin da aka yi amfanin da shi.

Abin da kawai akan ba mata shawara shi ne sai sun gwada kusan kowane kafin su san wanda ya fi karbar su. Hanya ta biyu ta rashin daukar ciki da ta shafi mace ita ce ta shayarwa. Mafi yawan mata (ba duka ba), ba su yin al’ada tsawon shayarwa - ko da kuwa tsawon shekara biyu suka shayar.

To a irin wannan yanayi ba su ba daukar ciki sai sun yaye.

Wannan dabara ba ta da wata matsala.
Sai kuma kirgen wata.

A kirgen wata mai gida zai kaurace wa ranakun
daukar ciki.

Wadannan ranaku su ne kwanakin tsakiyar watan matar – ba watanmu na lissafi ba.

Wannan kirge yana da ’yar rikitarwa, domin sai
mace ta tabbatar da cewa watanta ba ya rikici.
Sa’annan kuma yawancin magidanta ma ba su san mene ne kwanakin al’ada ba.

A irin wannan yanayi, dole maigida ya tambayi matarsa ta fahimtar da shi. Ga dan misalin kirgen wata: A mace mai kwanan wata 28, daga rana ta 9 zuwa goma sha 19 su ne ranakun tsakiyar wata wato ranakun da ake kyautata zaton daukar ciki.

A mai kwana 32, ranakun 11 zuwa 21 su ne ranakun kyautata zaton daukar
ciki.

A mafi yawan lokuta shi ma dai wannan bayani maigida da uwargida sai sun je asibiti ga likitansu ko ungozomar da aka ba horo, an ji karin shawara sa’annan bayanin ke fitowa dalla-dalla.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯
✎・・TOILET ✯ INFECTION ・・✎
☬ www.sirrinrikemijinki@yahoo.com ☬
☬ www.Sirrinrikemiji@gmail.com ☬
⚐ whatsApp
✎▻+2348037538596
▼・▼・▼・▼
▼・▼・▼
▼・▼

MAGANI CIWON SANYI ❖
✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯

Duk macen data ke son ni'ima ta tabbatar mata, koda yaushe ta kasance cikin ni'ima to lallai ya zama dole ta magance matsala ciwo sanyi.

( TOILET INFECTION)
✯✯✯✯✯✯✯✯✯
Domin magance wannan matsala ta samu wadannan kayan
✦ hulba
✦ bagaruwa
✦ habbatussauda
Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man habbatussauda kiyi matsi dashi.

❍ MAGANI SANYI ❍
✯✯✯✯✯✯✯✯✯
⁌ tafarnuwa
⁌ hulba
A bare tafarnuwa idan zaki kwanta bacci sai ki dauki saka daya ki yi matsi dashi ana son idan mace zata yi wannan hadin to miji ya daga mata kafa wato kada ya kusanceta
Da safe sai ta tafasa garin hulba ta zauna a ciki zata yi hakan har tsawon kwana uku
❖ RAGE KIBA DA TUMBI ❖
✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯
Ga masu dama da kiba ko tumbi wannan hadin na musamman ne wanda idan har kika hada shi to koda kina da kibarki zata a ganki kina aikace-aikace
▻ garin hulba
▻ ganyan na'a-na'a
▻ garin kanunfari
▻ zuma
▻ lemun tsami
▻ farin kwalli
▻ man na'a-na'a
Ki hade wadannan ganyen guri daya ki tafasa ki sami farin kwalli dunkulen zaki saka a ciki, idan ya kai kamar minti(5) sai ki cire,sannan ki saka zuma a cikin ruwan sha, ki samu na'a-na'a ki rinka shafawa TUMBI zai ragu insha Allah
Inda kuma ana son rage kiba ne za'a rinka zuba lemun tsami a ciki...
✧ GA MACEN DA TAKE ZUBAR Da JINI ✧
✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯
▻ saiwar magarya
A tafasata da yar ja kansa sai ki rinka sha
ZUBAR JININ
✯✯✯✯✯

∆ ganyan runhu
∆ balma
Sai ki hade su guri daya ki kika,ki sha , jinin zai tsaya da yardar Allah
❖ CIWON MARA ❖
✯✯✯✯✯✯✯✯
✑ tsamiya
✑ habbatussauda
✑ zuma
Ki sami tsamiya mai kyau da habbatussauda ki tafasa,ki zuba zuma a ciki/kisha shima za'a sami waraka
✎ GAME DA SAMUN HAIHUWA ✎
✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯
Matar da bata taba haihuwa ko kuma ta Dade ko ta sami tsawon lokaci bata haihu ba, sai ta sami kwan agwagwa guda ta soya. Amma man da zata soya wainar dashi man tafarnuwa a ciki ko kuma ta soya da man tafarnuwa sai tadi safe kafin tadi komai tayi haka a Jere kwana biyar zata sami haihuwa in Allah yaso
☼ WANDA BAYA IYA SADUWA DA IYALi ☼
✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯
fiye da sau daya(1)
Ko kuma ya soma sai ya gaji to
Sai ya sami dabino mai kyau, guda Dari da goma sha uku
Ya dafa da ruwa mai kyau
Idan ya tafasa sai ya tace
Da farko zai dafa ruwa kamar Kofi hudu,
Bayan ya tace sai ya Debi Kofi uku ya sake tafasawa yana cikin tafasa sai ya zuba man tafarnuwa babban cokali biyu,
Sai ya bashi akan wutar ta yadda ruwan zai dawo kamar Kofi biyu,
Idan ruwan ya huce sai ka rika sha babban cokali biyu sau hudu a rana , ya yi kwana (7) yana yin haka.
✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯

Post a Comment

0 Comments