AMFANIN KWAI WAJEN GYARAN FUSKA
📶 sirrin rike miji
☏+2348037538596
・ sirrinrikemiji@gmail.com
kurajen fuska na daya daga cikin ababen da ke bata fuska. Akwai wadansu kuraje masu yawan naci. Ya kamata mu kula da fuskarmu musamman ma lokacin damina saboda a lokacin ne fuska takan fitar da gishiri watau a Turance ‘sebum’, kamar yadda muka sani, gishirin fuska na toshe ramukan da gumi ke fitowa. Idan hakan ya faru, sai fuska ta fara yin kuraje.
Ababen da za a bukata:
MATAKAI:
Kwanuka biyu
• kwai daya
• Takardar ‘tissue’ daya
Amfanin kwai ga fuska:
• Ruwan kwai na da sinadarin gina jiki da sinadarin bitamin da kuma ‘minerals’
• Yana kare fuska daga kuraje.
• Yana kuma rage tsufar fuska.
• kara wa fuska haske.
•Rage kumburin ido.
A samu kwano daya sai a zuba ruwan zafi, wanda da shi ne za a turara fuskar. Kwano na biyu kuma sai a zuba ruwan kwai bayan an cire gwaiduwar, sannan a shafa ruwan ‘rose water’ saboda samun biyan bukata.
YADDA ZAKI HADA SHI:
•A fasa kwai sai a cire gwaiduwar.
•A kada farin ruwan kwan har sai ya yi kumfa.
• Daga nan sai a shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma a kan kurajen.
• A yagi takardar ‘tissue paper’ kadan, sai a manna a fuskar daga kan hanci har zuwa kumatu.
• A kara dora wata takardar ‘tissue paper’ a kan wanda aka manna a fuska tun a farko, watau hawa biyu kenan?
•Kada a yi dariya ko magana bayan an gama manna takardar ‘tissue paper’, domin yin hakan zai iya bude fuska, wadda kuma ana sanya takardar tissue paper din ne don ya matse fuska.
• Bayan hadin ya bushe, sai a wanke fuskar.
• Sannan sai a shafa gwaiduwar kwan a fuska na tsawon minti 15, sannan a wanke.
0 Comments