✎ MAGANIN CIWON SANYI DA MAGANIN SA●
*● TOILET INFECTION ●*
☏+2348037538596
✎ KAIKAIYIN GABA:
sirrinrikemiji@gmail.com
sirinrikemiji@gmail.com
・・Ma'anar sa:-
TOILET INFECTION
wata cuta ce da take samun mace da namiji, cuta ce wadda take a cikin mace da kuma gaban ta.
Cuta ce wadda wani zai iya daukar ta daga wani, za'a iya daukar ta idan wata tayi fitsari a daidai wani wuri kema sai kije kiyi, za kuma ki iya daukar ta ta hanyar sharing pants da wadda take dashi. Haka kuma ana iya daukar shi a yayin saduwa (sex), mace zata iya gogawa namiji haka namijin ma zai iya gogawa mace shi.
Idan na kasa mata kashi dari tou fa 95% suna da wannan cutar. Cuta ce mai matukar wahalar magani ga wanda basu san yanda zasu magance shiba.
Tambaya anan itace:- shin me yasa mutanen da basu san miye.
● *TOILET INFECTION* ba?
Me yasa babu shi a baya?
Nikam a gani na hakan ya faru ne a dalilin yawan inserting da matan mu na yanzu keyi, matan da basu san miye cushe-cushe a gaba ba, yanzu ne abun yayi yawa. Idan ma zakiyi inserting din sai kisan abunda zakiyi dashi. Taya zaki mayar da vigina din ki tamkar wata bola? Duk abunda kikaga dama ki zuba a ciki kuma kisa ran zaki zauna lafiya? Hakan ba mai yiwuwa bane a gani na.
*● ABUBUWAN DA TOILET INFECTION YAKE HAIFARWA ●*
☏+2348037538596
● rashin gamsar wa a yayin jima'i.
● rashin haihuwa.
● rikicewar al'adah.
● soshe-soshen gaba a cikin mutane, har wasu su ringa k'yamar ki da abun hannun ki.
● ALAMOMIN TOILET INFECTION ●
☏+2348037538596
⇀ fitar farin ruwa.
⇀ rikicewar al'adah.
⇀ kaikayin gaba.
⇀ gaba ya ringa yin zafi a yayin yin fitsari.
⇀ jin tsirar gaba ba tare da dalili ba.
⇀ yin fitsari guntu-guntu.
● HANYOYIN MAGANCE TOILET INFECTION ●
☏+2348037538596
✎ Ki daina inserting ko wane irin magani a gaban ki, sai miski, duk wata kawa ko yar uwarki da zata baki wata shawara akan ki matsa wani abu yana karin ni'imah kar kiyi wallahi, ki bata shawara itama tayi kokarin dainawa.
● ki ringa tsarki da warm water, (not too hot water dan kar ya sale ki..
● ki ringa inserting da miski a koda yaushe, yana warkar da wannan cutar sosai.
● ki ringa shan maganin bature (tabs) saboda shi zai kashe miki na cikin.
● ki jika ruwan lalle amma kar ki cika lallen da yawa, sai ki zuba zuma kadan a ciki, ki ringa shan cokali uku ko wace rana, shima zai kashe miki na cikin ki sosai.
Saboda ko kinyi magani na kasan ki indai kina da na cikin tou akwai matsala, saboda ciwon yana nan.
● HANYOYIN DA ZAKI BI YAYIN YIN MAGANIN TOILET INFECTION ●
☏+2348037538596
✎ ki wanke pants din ki da ruwan zafin da kika tafasa shi da gishiri, ki shanya su a rana har sai sun bugu sosai (idan so samu ne ma duka ki yarda su ki sake wasu).
✎ duk maganin da zaki sha ya zamana mijin kima yana sha, idan kina da kishiyoyi suma susha, saboda ko kin sha magani kin warke aikin banza ne Indai suna dashi.
✎ ki daina kwana da pant a yayin yin maganin shi, saboda ana bukatar iska ya yawaita shigar ki.
⟳ MAGANIN WARIN GABA ⟳
☏+2348037538596
☞ ki kiyaye wajen yin tsarki idan kikai bahaya sai ki koma gefe daya kiyi tsarki.
☞ amfani da miski.
☞ yawan tsarki da ruwan dumi.
☞ ki dinga tsarki da ruwan dumi.
☞ zama da wando a ko wane lokaci.
☛ tsaftace bandaki da lura da shi akai-akai dan kaucewa daukar cutar bandaki.
● SIRRIN KARAWA MACE SHA'AWA ●
☏+2348037538596
akwai mata da dama da zaka samu sha'awa su ta dauke yawancin su matan aure ne sune suka fi samu wannan matsala, wanda zaka samu sun yin jima'i ne kawai domin raya sunna amma bawai domin suna jin dadinsa ba
Don haka yar'uwa ga wata fa'Ida DA zaki gwada ko ALLAH zai saka a dace.
❛ zogale
❛ kanunfari.
zaki nika zogelenki kitace ruwansa sai ki zuba masa kanunfari ki dinga sha safe da yamma.
● MAGANIN NARKARWA ( TABO) ●
ȏ.̮ man kadanya
ȏ man zaitun
ȏ.̮man dodon kodi
ȏ lemon tsami.
Ki hada man duka a waje daya sai ki matse lemon tsami ki juya sosai ki dinga diba kina shafawa a wajen.
✧ TABON FUSKA ✧
▽ zaitun soap.
▽ anoconda soap.
▽ pharmadan soap.
▽zuma soap.
▽ kanwa.
∇ Lemon tsami.
A hadasu waje daya a cikin turmin karfe Ki kirba su sai ki zuba a cikin wata roba ki dinga wanke fuska DA shi safe da yamma.
● TABO DA KURAJEN FUSKA ●
ki samu ganyen dogon yaro sai ki hada shi DA kurkum a hada sai ki shafa a fuska bayan kamar minti 15 sai ki wanke fuksar DA ruwan dumi.
✎ SABULUN TSARKI ●
♜ bagaruwa
♜ zaitun soap zaplan
♜ farin miski
♜ hulba
Su zaki hada ki kwaba sannan ki dinga yin tsarki kina wanke gabanki DA shi hakan zai taimaka miki wajen kawar da warin gaba MACE.
■ TSARKI BAYAN KIN KAMALA HAILA ■
akan so idan kika kamala jinin haila ki samu:
⇨ ganyen magarya.
⇨ miski.
⇨ garuwa kadan.
⇨ kanunfari.
Sai ki hada su ki tafasa idan Ya kamala huce sai ki samu detol kadan ki zuba a ciki sai ki shiga ciki ki zauna.
♜ bayan Nan sai ki samu:
⇨ zuma.
⇨ miski.
Kiyi inserting.
■ SABON HADI ■
♜ lemon zaki
♜ madara ta ruwa
♜ zuma.
Ki matse lemon sai ki kawo madara ruwa ki zuba zumarki shima wannan hadin ki hada shi kiji yar'uwa.
☛ HADIN GYADA ✰
wannan hadin yana sakawa ko wane lokaci maigida ya zama yana mane dake da farko zaki samu:
♧ gyada
♧ zuma
Ki samu gyadar ki sai ki hada ta waje daya bayan kin gyara sai ki markada sannan kuma sai ki tace ta daga Nan sai ki kawo zuma ki zuba sai ki daukota ki saka a firji bayan wani lokaci ki daukota ki yini kina sha yar'uwa wannan hadin yana da ban mamaki sai ki hada kinji.
●••RASHIN GAMSAR DA MAIGIDA••●
idan har bakya gamsar da mijinki a yayin rayuwar aure sai ki nemi.
♙ furen tumfafiya
♙ ya'yan zogale
♙ gero.
Sai ki hada su ki dake su luki ki dinga sha da fresh milk.
❀❀ MATSI GABA ¹❀❀
♡ garin zogale
♡ karo
♡ man kadanya
♡ man shanu
A samu garin zogale a busar da shi a hada su a kwaba a dinga yin matsi.
✰ MATSI GABA 2 ✰
♤ bagaruwa
♡ alif
♤ ganyen magarya.
A tafasa su a dinga shiga cikin ruwa..
0 Comments