#tsangayanmalam
Ma'aurata musamman ma sabbin shiga. Suna saurin samun matsala a aurensu ne saboda rashin masu basu shawara ko Kuma rashin daukan shi kansa shawaran bayan an basu ita.
Ga wasu shawarwari nan da idan ma'aurata suka yi amfani da su suna iya samun Zamantakewan aure mai inganci. Waɗannan shawarwarin wasunsu ba wasu sabbi bane amma saboda ingancin amfani dasu a tsakanin ma'aurata ake ta nanatasu kamar haka;
1: Sadarwa: abu na farko kuma mai mahimmanci da yake inganta zaman aure shine sadarwa a tsakanin ma'auratan.
Duk abunda guda ya gani ko yaji da bai gane ko fahimta ba yanada kyau yayi ƙoƙarin neman bayani. Kada wanda yayi wani al'amari cikin zato ga gudan. Yi tamabaya idan ba a gane ba.
2: Yin Shawara: duk ma'auratan da suke zama su shawarta matsalolin gabansu, da kuma abubuwan da suke son aiwatarwa akan 'ya'yan su ko iyalansu ba za a taɓa jin kansu ba.
3: Kalmomin Soyayya: daga lokacin da aka gama cin amarci daga wannan lokacin wasu ma'auratan sun dai furtawa junansu kalaman soyayya. Bare kuma ace sun haihu shi kenan.
Furtawa juna kalaman tsoyayya yana kara danƙon ƙauna ga ma'auarata komai tsufansu. Don haka ba abun kunya bane nunawa junanku ƙaunar dake tsakaninku ta hanyar furuci ko abunda yayi kama da hakan.
4: Uzuri: baiwa juna uzuri yanada tasiri a zaman aure.
Kada ma'aurata su kasance masu saurin yanke hukunci ba tare da bada uzuri ba. Duk abunda aka yi a ɗauka ba haka bane har sai an tabbatar da hakan ne.
5: Zargi: ɗabi'ace dake saurin ruguza aure. Dole ne ma'aurta su baiwa junansu yarda 100/100. Hakan zai basu damar amincewa juna, tare kuma da doɗe duk wata ƙofar munafurci da za a yi ƙokarin shiga tsakaninsu.
6: Kada Ku Aibata Junanku: kada ku sake ku aibata junanku a wajen mutane na waje. Kada a taɓa jin cewa guda daga cikin ku ya taɓa zuwa ya aibata guda a wani wajen.
7: Kada Ku Bada Dama: kada ma'aurata su sake su baiwa wasu 'yan uwa ko abokai fahimtar tsalar data gifto a tsakaninsu.
Koda suna tsaka da wata matsalar ce suna jin anyi sallama to su maida komai ba komai bane a fuskarsu da kuma zukatansu.
Yawaita barin ana shiga tsakani ko nunawa wasu ɓacin rai na laifin da aka yiwa juna na iya ruruta matsalar maimakon gyara saboda ba koya zai fadi alheri ba.
8: Kada Ku Tsammaci Daidai: ku sani dukkaninku 'yan adam ne, ba kullum kuma ba a komai zaku iya yiwa juna daidai ba. Don haka saka hakan a rai zai hana yawan yin fushi na haka nan kawai.
9: Karantar Juna: dole ne ma'aurata su karanci junansu yadda zasu iya fahimtar juna da motsa giran ido kaɗai.
Fahimtar juna ga ma'aurata yana sa su gano abubuwan da suke so a musu da abunda basa so. Wanda da zara wani cikinsu yayi ba daidai ba ya sani ba ma sai an furta ba.
10: Wayar Hannu: duk ma'auratan da suke son ganin ingancin zaman aurensu su guji bincike a wayoyin junansu.
Yin hakan ba wai yana nufin akwai abunda suke aikawata da ba daidai bane. Sai dai saboda yarda da amincin da suka riga suka yiwa junansu na babu abun na rashin gaskiya da zasu yi ko su boyewa junansu.
Baya ga hakan daga lokacin da ma'aurata suka bari zuciyarsu ta raya musu su binciki wayan juna, daga wannan lokacin fatan samun matsala yazo. Duk ƙanƙantar matsalar da aka samu tana iya zama babba saboda daman da tunanin rashin yarda aka shiga binciken.
Dafatan za a yi amfani da shawarwarin.
0 Comments